DANGANTAKA DA AURATAYYA TSAKANIN AHALUL BAITI DA - TopicsExpress



          

DANGANTAKA DA AURATAYYA TSAKANIN AHALUL BAITI DA SAHABBAI Wallafar: Shaikh Prof. Umar Muhammad Labdo *** Darasi Na Ashirin Da Shida (26) *** =========================== NASABA DA SEREKUTAR UMAR BINUL KHADDAB(RA) Shi ne Umar dan Khaddabi dan Nufail dan Abdul Uzza dan Rayah dan Abdullahi dan Qurdi dan Razahi dan Adiyyu dan Ka’abu dan Luayyu dan Galib dan Fihiru. Ya fito daga gidan Banu Adiyy. Nasabarsa na hadewa da Annabi(SAW) a kan kakansa na bakwai, Adiyyu dan Ka’abu. Umar yana cikin Musulmin farko; ya musulunta a lokacin da Annabi(SAW) yake gidan Arqam. Allah ya daukaka addini da musuluntarsa, a yayinda Musulmi suka numfasa kuma suka fito fili suka nuna addininsu a Makka. Ya lizimci Annabi(SAW) a tsawon rayuwarsa, ya halarci dukkan yakoka tare da shi kuma ya sadaukar da rayuwarsa da duk abinda ya mallaka wajen yada addinin Musulunci. Ya aurawa Annabi(SAW) diyarsa Hafsa(RA) kuma ya zama Khalifansa na biyu bayan Abubakar(RA). Sarkin Musulmi Umar gwarzon namiji ne wanda ya jagoranci rundunonin Musulunci wajen rusa daulolin Farisa da Rum. Ya cinye kasashen Iraqi da Farisa da Sham da Misira da wasunsu. Ya kafa durakun daular Musulunci, ya assasa tsaretsaren mulki masu kyau kuma ya shimfida adalci. Umar ya yi shahada a shekara ta bayan hijira, yana da shekaru sittin a duniya. Abu Lu’uluatal Majusi, wanda bamajusen Farisa ne aka kamo shi a yaki yake zaman bauta a Madina, shi ne ya kashe shi domin daukar fansar rushe daular Majusawan Farisa da Khalifan ya yi. Wannan bamajuse a yau yana da hubbare a kasar Iran wacce ‘yan Shi’a daga ko ina a duniya suke ziyarta domin girmamawa. Umar(RA) ya auri mata da dama. Sun hada da: (1) Zainab diyar Maz’un dan Habib, ‘yar uwar mashahurin Sahabin nan Usmanu binu Maz’un, ta haifa masa Hafsa Innar Muminai matar Manzon Allah(SAW), da Abdullahi. Wadannan su suka fi shahara cikin diyan Umar. (2) Ummu Kulthum diyar Ali da Fadima, ta haifa masa Zaid da Ruqayya. Watau Umar ya aurawa Annabi(SAW) diya kuma ya auri jikanyar Manzon Allah(SAW). Wannan auratayya da ta je ta zo tsakanin Umar da Ma’aiki, tana nuna dangantaka tsakanin Banu Adiyy, dangin Umar, da Ahalul Baiti. Kuma koda yake ma’abota jahilci, masu batan bakatantan, suna cewa kwatar Ummu Kulthum Umar ya yi, amma duk mai hankali da addini ya san Sahabin Annabi bai kwatar mace ya zauna da ita ta haifa masa ‘ya’ya, koda yana iya yin hakan, kamar yadda ya san cewa ba’a iya kwatar diyar Ali(RA) koda kwacen ya zama al’ada a tsakaninsu. Saboda haka, Ali(RA) ya aurawa Umar(RA) diyarsa Ummu Kulthum a kan yardarsa da son ransa, saboda soyayya da kauna da ban girma dake tsakaninsu. Kuma mene ne abin mamaki idan Ali ya aurawa Umar diyarsa? Shin Annabi(SAW) bai auri diyar Umar ba? Bayan rasuwar Umar, Ummu Kulthum ta auri Aunu dan Ja’afar binu Abi Dalib, ya rasu ta yi masa takaba. Bayan rasuwarsa, ta auri dan uwansa, Muhammad dan Ja’afar binu Abi Dalib, shi ma ya rasu ta yi masa takaba. Sa’an nan ta auri dan uwansa har yau Abdullahi dan Ja’afar binu Abi Dalib wanda ta rasu a gidansa. Banda wadan nan mata biyu, Umar ya auri wasu mata da dama, kamar Ummu Hakim diyar Harith ta Banu Makhzum da Jamila diyar Thabit Ba’ansariya da Atika diyar Zaid. In sha Allah, a darasi na gaba za mu ji, Nasaba Da Serakutar Usman Binu Affan(RA).
Posted on: Sun, 26 Jan 2014 20:42:26 +0000

Trending Topics



dy" style="min-height:30px;">
“We tell them they can do anything, they can be anybody, but if
O CONCURSO Um grupo de cientistas estava discutindo qual deles
I will be starting a brand new Wing Chun Kung Fu class @ Venue to
En esta entrega de la mítica saga de Star Trek, dirigida por el

Recently Viewed Topics




© 2015