Daga Saifullahi M. Kabir YUNKURIN GOODLUCK EBELE JONATHAN NA - TopicsExpress



          

Daga Saifullahi M. Kabir YUNKURIN GOODLUCK EBELE JONATHAN NA KASHE SHEIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H); SABON SHIRI NE NA KARISA RUGUZA ZAMAN LAFIYAR NIGERIA. Daga Saifullahi M. Kabir Wani abin mamaki, a duk fadin kasar Nigeria an rasa samun wani babba; imma dan siyasa ko mai sarautan gargajiya, ko kuma Malami da zai iya sallama rayuwarsa wajen tona asirin wannan taaddancin da Jonathan tare da jamiansa suke aikatawa tsawon shekara hudu da sunan BOKO HARAM sai Sheikh Ibraheem Yaqoub al-Zakzaky. Allah ya sakawa Malam Zakzaky da dukkan alkairansa, ko mutum baya sonsa, zai yi shaida akan cewa tun a zamanin Ummaru Musa Yar Adua, wanda shine farkon asasin Boko Haram, da suka fara wannan Drama din nasu da sunan wata kungiyar Sunnah mai nufin tabbatar da Musulunci na fada da gwamnatin Nigeria. Sheikh Zakzaky yace; Wannan karya ne, rainin hankali ne, wasu zaku ruda ba mu ba, shiri ne na rusa zaman lafiyar kasar nan kamar yadda Amurka suka ce Nigeria zata wargaje zuwa 2015. Ku dubi yadda Sheikh Zakzaky ya yi ta bayyana cewa wani shafi na Internet da wasu Amurkawa ke tafi da shi, sun rubuta karara cewa zuwa 2015 akwai yiwuwar Nigeria zata hargitse. Sukace kuma Nigeria zata zama bata da tsayayyen shugabanci (wato, zai zama Shugaban kasar ta fanko ne, daga wani wajen ake control din tafiyar kasar). Sukace akwai yiwuwar shigowar Amurka Nigeria saboda dalilai biyu; 1- A Nigeria akwai maadanai (albarkatun karkashin kasa) da suka hada da mai da sauransu. A lokacin Sheikh Zakzaky yake cewa; ba mamaki kuwa zasu iya zuwa saboda wannan din, domin shi ya kaisu Iraq, shine dalilin da yasa suka yaki Afganistan, dss. Kuma Sheikh din ya ba da misali da kasar Somalia wacce kwata-kwata albarkar da suke da shi na kasa shine suna da kifaye masu kyau. Amma saboda kifi Amurka ta saka su a wannan halin da suke ciki, yau kusan shekaru 20 basu zaune lafiya. Kullum tashin hankali da yunwa, sai mutuwa kawai ake. 2- Dalili na biyu da Amurkawa suka bayyana wanda zai iya kawo su Nigeria, shine zasu zo su yaki Motsin Musulunci (Islamic Movement) wanda kamar yadda suka rubuta a site din cewa, Led by Mr. El-Zakzaky, wato wacce Malam Zakzaky kewa Jagoranci. Sunga wannan Harkar ta Musulunci a matsayin barazanarsu ne saboda sun san cewa tafiya ce mai hadarin gaske garesu, wacce irinta ce suka rainata a kasar Iran kuma tazo ta basu mamaki, yayin da ta kasa tsayayyiyar daular Musulunci, kuma har yau suka gagara takata duk da kullum yunkurin hakan suke yi. Wadannan duk Sheikh Zakzaky ya ta bayyana su a jawabansa, tun a shekarar 2009 zuwa 2010. Inda ya yi ta bayyana cewa BOKO HARAM wani plan ne na yakar alummar Nigeria, kuma hukuma ce ta kirkireta, su ke dramarsu da kansu, kuma babban target din hukumar shine Harkar Musulunci da ke razana su. Ba lokacin da zaa saka bomb ko akai wani hari (irin wanda BBC sukance Yan Kunan bakin wake, ko mahara ko yan bindiga dadi din nan) face Sheikh Zakzaky yace Hukumar Kasar nan ce da alhakin kai wannan harin. Abin mamaki; maganarsa a public yake yi, kuma jaridu sukan dauka su buga, da ma tasoshin Talabijin, da sauransu. Amma ko sau daya baa taba samun lokacin da hukumar Nigeria ta fito, ta bakin wani jamiinta na siyasa ko ta bakin soji ko yan Sanda da suni kare kansu daga wannan zargin da Sheikh Ibraheem Zakzaky ke musu. Naam, ni ban yi imani da cewa zargi bane, nayi imani da cewa reality ne yake fada, ba shaci-fadi bane. Domin naga wani Babban Malamin addini a bangaren Izala da ya yi subul da baka akan wani babban Azzalumi (Gen. Almustapha), wanda Almustapha tsohon dogarin Dolo da bindiga (Gen. Abacha) ne, yanzu shi ba hukuma bane, amma take ya kai wannan malamin Kungiyar kotu, abin da ya tilasta masa fitowa ya karyata kansa a gaban jamaa ko yasha dauri. To me yasa hukumar kasar nan bata fitowa ta nemi yancinta idan Sheikh Zakzaky yana ci mata ne ta hanyar jingina mata abin da bata da alhakinsa? Aikinsu kenan yunkurin kisa; Zasuyi kisa - Zasuyi kisa... Abin da ke kara fito mana da abin fili cewa sun tabbatar su suke yi, kuma basu bukatar wani da baya tsoronsu da zai bayyana ma alumma su suke yi din. Sun rasa karfin halin suyi abu su bugi kirji suce su sukai har yanzu. A baya-bayan nan: 1- SACE YAN MATAN CHIBOK: Sai da aka sace su da kwanaki goma sha, sannan Ebele Jonathan a matsayinsa na Shugaban Kasar Nigeria ya fito ya yi magana akai. Duk da cewa mata ne, aka sace su sama da dari biyu da hamsin, kuma a makarantar boko. Sannan drama din da Hukumar kasar nan suka rika acting a kan lamarin yan matan Chibuk, sai da ya bayyana ma duk alummar kasar nan cewa jamian Jonathan ne suka sace wadannan yan matan. Da tsakar rana, a tsakar waje, a gaban dubban daruruwan alumma, Sheikh Ibraheem Zakzaky yace; In dagaske ne ana neman yan matan Chibuk a neme su ne a wajen Jonathan, shi yasan barikin da yake aje da su. Sheikh din ya kara da cewa; Ba wata tsiya wai ita Boko Haram, ba mune zakuma wannan Iskancin ba!. Duk wadannan maganganun da Sheikh Zakzaky keyi, sai da aka samu gidajen Jaridu da tashoshin Radio (da FM) da gidajen TV sama da 30 wadanda suka kawo rahoton, amma har yau Jonathan ko Jamiinsa na siyasa ko na tsaro, basu fito sun kare kansu akan hakan ba. Sai ma suka dauki matakin kaima Sheikh din hari a farkon Ramadan, wanda hakarsu bata cimma ruwa ba, suka jinkirta zuwa karshen Ramadan din. 2- KASHE SHEIKH AUWAL ALBANI ZARIA: Sheikh Zakzaky (H) a fili ya bayyana ko su waye makasan Albani, har yace kuma su almajiransa sun san ko suwa suka kashe shi, zasu kame bakinsu ne kawai saboda tsoro. Sheikh din yace amma mukam bama tsoron kowa! Abin mamaki, Jonathan ta hannun jamiansa sun kashe Sheikh Albani da iyalansa wadanda basu ci musu ba basu sha musu ba, koda ace shi Sheikh Albani ya musu lefi me iyalinsa sukayi kuma? Amma dai an kashe su. Shima kuma bayan kashe sun aka so ayi amfani da hakan wajen yamutsa kasar, Allah (T) mai tausayi da jinkai ya kiyaye. 3- KAI MA SHEHU DAHIRU BAUCHI HARI: An kai a ranar Laraba da safe, da yamma a wajen Tafsirin Al-Qurani, Sheikh Zakzaky ya bayyana cewa hukumar kasar nan ce takai hari akan Shehu Dahiru Bauchi da Janaral Buhari. Nasan har daya daga wadanda aka kaima harin ma tsoro yasa ya furta wata mara kan gadon magana, inda yake cewa ba daya daga mutanensu da harin ya shafa, amma kuma shedun idanu sun nuna kusan mutum 30 ne suka rasu a harin. Amma Sheikh Zakzaky ya bayyana Jonathan ne da wannan aikin. Babban matakin da hukumar kasar nan zasu iya dauka dangane da tona asirinsu da Sheikh Zakzaky ya yi na hare-haren da suke kaiwa shine Yunkurin ganin bayansa ta hanyar kisa. Shi yasa kwanaki biyu bayan harin da suka kaima Sheikh Dahiru Bauchi da Janar Buhari, Sojojin Nigeria da tsakar rana a idon jamaa suka bude ma masu zanga-zangar lumana don nuna goyon baya ga alummar Palastinu wuta, suka kashe mutane 34 ciki har da yaran Sheikh Zakzaky, wanda sun kama su da ransu ne suka harbe su daga baya. Cikin wadanda suka kashe har da wani Dattijo 68, Kirista, dan kabilar Igbo. Da mata da kananan yara, da dalibai yan Jamia. Kuma suka raunata sama da mutum dari da ashirin. Sannan tun daga lokacin har yau ba hakura sukai ba, kullum Jamian tsaron Nigeria, musamman Sojoji a Karkashin Commander Bassawa Barrack, S.O Oku, suna karkashin target ne na kashe Sheikh Ibraheem Zakzaky. Kullum yunkurinsu kenan. Sai muka ji wani labari, ita Hukumar kasar an bata umurni daga waje, akan ta gama da Sheikh Zakzaky ta hanyar kashe shi nan da wata daya. Kuma yanzu haka an kai kusan kwana 10 amma kisan bai yiwu ba. To muna tabbatar muku da ba zai taba yiwuwa ku kashe shi ba har sai lokacinsa ya yi. Duk abin da kuke iyawa kuyi, baku isa ku kashe shi ba sai sadda ajalinsa ya cika. Naam. Bayaga kokarin ganin bayan Malam Zakzaky da Jonathan da Namadi Sambo suke yi saboda shi barazana ne ga tafiyarsu da na iyayen gijinsu. Har wala yau, suna da burin cinma nasarar wargaza zaman lafiyar kasar Nigeria ta yadda sam ba zaai sabe ba a 2015 din nan, sakamakon hargitsewan kasar, sai su cigaba da satan kudaden da suke.... Wannan zanyi bayaninsa a rubutu na gaba Insha Allah.
Posted on: Sun, 16 Nov 2014 09:09:42 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015