Daga Ummu Abdillah Zaria. العقيدة الصّحيحة وما - TopicsExpress



          

Daga Ummu Abdillah Zaria. العقيدة الصّحيحة وما يضادّها INGANTACIYAR AKIDA DA KISHIYARTA //04 (2) IMANI DA MALA’IKU : Na biyu cikin Ginshikan Imani shi ne Imani da Mala’iku. Imani da Mala’iku ya kunshi Imani da su a dunkule da kuma daki-daki. Shi ne musulmi ya yi imani cewa, Allah Yana da Mala’iku wadanda Ya halicce su don su bauta maSa, Ya kuma sifanta su da cewa su bayi ne ababan girmamawa, ba sa gabatarSa da magana, kuma su da umarninsa suke aiki. Allah Ya ce : « Yana sanin abin da yake gare su, da abin da yake a bayansu, kuma ba su yin ceto face ga wanda Ya yarda, kuma su masu sauna ne saboda tsoronSa » [Al-Anbiya’i, aya ta 28]. Su Mala’iku dangogi ne masu yawa, a cikinsu akwai wadanda aka wakkala musu daukan Al’arshi, a cikinsu kuma akwai masu tsaron Aljanna da Wuta, a cikinsu kuma akwai wadanda ake wakkala musu kiyaye aiyukan bayi. Kuma muna yin Imani da duk Mala’ikun da Allah ManzanSa suka ambace su, kamar Jibrilu, da Mika’ilu, da Malik, mai tsaron Wuta, da Israfilu, wanda aka wakilta shi da busa kaho. Ambaton wadannan ya zo a cikin hadisai ingantattu. Kuma ya zo a cikin wani ingantaccen Hadisi daga A’isha, Allah ya yarda da ita, cewa Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce : “ An halicci Mala’iku daga haske, an halicci Aljanu daga harshen wuta, an kuma halicci Adam daga abin da aka sifanta muku” Muslim ya ruwaito shi a cikin Sahihinsa. (3) IMANI DA LITTATTAFAI : Na uku cikin Ginshikan Imani shi ne Imani da Littattafai. Wajibi ne a yi Imani da littattafai a jumlance, a yi Imani cewa Allah, Tsarki ya tabbata gare Shi, hakika ya saukar da Littattafai ga AnnabawanSa da ManzaninSa, don su yi bayani hakkin Allah a kan bayi, kuma su yi kira zuwa gare Shi, kamar yadda Allah Madaukaki Ya ce : « Hakika, lallai Mun aiko ManzanninMu da hujjoji bayyanannu, kuma Mukaa saukar da Littafi da ma’auni tare da su, domin mutane su tsayu da adalci » [Al-Hadid, aya ta 25]. Kuma Allah Madaukaki Ya ce : « Mutane sun kasance al’umma guda. Sai Allah Ya aiki Annabawa, suna masu bayar da bishara, kuma masu gargadi, kuma Ya saukar da Littafi da gaskiya tare da su, domin (Littafin) ya yi hukunci a tsakaninsu mutane, a cikin abin da suka saba wa juna a ciki » [Bakara, aya ta 213]. Mun kuma yi Imani da Littattafan nan da Allah Ya ambace su daki-daki, kamar Attaura, da Linjila, da Zabura, da Alkur’ani. Mun kuma yi Imani cewa Alkur’ani shi ne fiyayyen wadannan Littattafai, kuma shi ne cikamakinsu. Kuma shi mai shaida ne a kansu, kuma mai gaskatawa ne a gare su. Kuma shi ne yake wajibi a kan dukkan al’umma su bi shi, su kuma hukunta shi a kansu, tare da abin da ya inganta na Sunnah da ta zo daga Manzon Allah, tsira da aminin Allah su tabbata a gare shi. Saboa Allah, Tsarki ya tabbata gare Shi, Shi ne Ya aiko ManzonSa Muhammad, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, zuwa ga nauyaya biyu (mutane da aljanu), kuma Ya saukar da wannan Alkur’ani, domin ya yi hukunci da shi tsakaninsu, Ya kuma sanya Alkur’ani ya zama waraka ga duk abin da ke cikin zukata, da kuma bayani ga kowane abu, da kuma shiriya da jin-kai ga muminai. Kamar yadda Allah Madaukaki Ya ce : « Kuma wannan Littafi ne, Mun saukar da shi mai albarka ne, sai ku bi shi kuma ku yi takawa, tsammaninku, ana jin-kanku » [Al-An’am, aya ta 155]. Kuma Allah, Tsarki ya tabbata gare Shi, Ya ce : « Kuma Mun sassaukar da Littafi a kanka domin yin bayani ga dukkan komai, da shiriya da rahama da bushara ga masu mika wuya (Musulmi) » [Al-Nahl, aya ta 89]. Kuma Allah Madaukaki Ya ce : « Ka ce : “Ya ku mutane! Lallai ne ni Manzon Allah ne zuwa gare ku, gaba daya. (Allah) wanda Yake Shi ne da mulkin sammai da kasa, babu wani abin bautawa face Shi, Yana rayarwa, kuma Yana matarwa, sai ku yi Imani da Allah da ManzonSa, Annabi, Ummiyyi, wanda yake yin Imani da Allah da kalmominSa, kuma ku bi shi ko kwa shiryu” » [Al-A’araf, aya a 158]. Ayoyin da suka zo da wannan ma’ana suna da yawa. (4) IMANI DA MANZANNI : Na hudu cikin Ginshikan Imani shi ne Imani da Manzanni. Yana wajaba a yi Imani da Manzanni a jumlance, da kuma daki-daki. Wajibi ne mu yi Imani cewa Allah Madaukaki Ya aiko zuwa ga bayinSa
Posted on: Sun, 14 Jul 2013 16:32:37 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015