Dr. Mansur Sokoto ME YA FARU A KARBALA 13 Yarima Ya Zama - TopicsExpress



          

Dr. Mansur Sokoto ME YA FARU A KARBALA 13 Yarima Ya Zama Sarki Tun daga hudubar farko da Yazid ya yi ya fara sauya siyasar mulki daga ta babansa kamar yadda hausawa suka ce, Sarki Goma Zamani Goma. Yazid ya soma da jajanta ma jamaa game da mutuwar sarkin musulmi Muawiyah a cikin hudubarsa, sannan ya bada sanarwar biyan albashi na wata uku a game (a wancan lokaci talaka albashi gwamnati take yi masa. Sunnar da sayyadi Umar dan khattabi (R.A) ya fara). Sannan Yazidu ya ce ya dakatar da yaki a bangaren teku saboda gabatowar lokacin sanyi. Daga juyayi sai mutane suka koma murna. Ba a birnin Sham kawai aka yi wa Yazidu mubayaa ba. Aa har da Makka da Madina da Masar da sauran garuruwan musulmi. Amma mutane biyu da muka sani cewa ba su yi mubayaa ba tun wuri ayyana Yarima suna nan a kan matsayinsu. Kuma ganin kamar gwamnan Madina Al-Walid bn Utbah zai yi yunkurin tilasta su sai suka sauya mazauni su biyun daga Madina suka koma Makka. Husaini (R.A) ya kwashe duk iyalansa ya tafi da su in ban da kanensa Muhammad bn Ali (Ibnul Hanafiyyah) shi kam daman ya yi mubayaa kuma ya shawarci wansa Husaini da ya canja raayi shi ma ya yi. Ya ce, shi bai ga dalilin da musulmi zasu hadu a kan wani mutum ba sannan a ki amincewa da shi.
Posted on: Thu, 24 Oct 2013 14:03:28 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015