HANYA INGANTACCIYA DA TA DACE DA SHARI’AH ///22 **TUNTUBE DA - TopicsExpress



          

HANYA INGANTACCIYA DA TA DACE DA SHARI’AH ///22 **TUNTUBE DA KURAKURAN WASU MALAMAN TAFSIRI (5)** Cigaba: Irin wannan tuntube ma ya sami Annabi Yunusa (AS), inda ya yi wa jama’arsa wa’azi suka ki karba sai ya yi fushi da su. Da ya shiga jirgi zai yi kaura, sai jirgin ya fara tambal-tambal zai kife da su, sai masu jirgin suka ce, “Idan aka rage mutum daya to jirgin zai tafi daidai.” Sai aka yi kuri’a kuma kuri’ar ta fado kan Annabi Yunusa sai nan take ya fada cikin ruwa sai kifi ya hadiye shi, daga nan sai ya rika cewa, «Ba wani abin bautawa da gaskiya sai kai Allah, tsarki yatabbata a gare Ka, hakika ni na kasance cikin azzalumai ». Allah Ya ce, «Sai muka amsa masa, kuma muka tserar da Muminai » (Anbiya’i : 88). Kuskuren da Annabi Yunusa ya yi shi ne yin fushi da mutanensa da suka kafirce wa Allah, sai Allah Ya ce ya koma gare su, kuma ya koma aka aika da shi cikin mutanen sama da dubu dari kuma suka yi imani da shi. Haka kuma, irin wannan ma ya sami Annabi Nuhu (AS), inda aka halakar da Dansa mai suna Khan’ana. Annabi Nuhu yana cewa, «Ya Ubangiji lallai dana yana daga cikin iyalaina kuma alkawarinka gaskiya ne, don kuwa kai ne fiyayyen masu hukunci» Sai Allah Mai girma Ya ce wa Annabi Nuhu, «Ya kai Nuhu, shi ba ya cikin iyalanka, ba ka ga aikin da ya yi mummuna ne ba? Kada ka tambaye ni abin da ba ka da ilimi a cikinsa» (Hudu : 45-48). Irin wannan kuma ya sami Annabi Yusuf (AS), a lokacin da ya gayawa wani da aka daure su tare a gidan kurkuku, inda ya ce ka ambace ni a wajen mai gidanka sai Shaidan ya mantar da shi wannan sako na Annabi Yusuf har ya zauna a cikin kurkuku kusan shekara goma. To irin wadannan kurakurai su ne ya kamata a raba su wato a dinga dangana su a cikin Tafsirin wannan aya, «Ba mu aiko wani Manzo ko wani Annabi ba, sai idan ya yi burin isar da sako na Allah, sai Shaidan ya sa masa wata dimuwa, kafin ya isar da wannan dimuwar da Shaidan ya jefa, sai Allah Ya daidaita wannan sakon da Yake so ya isar, sai Manzon ya isar da sakon daidai ba dadi ba ragi, don Allah masani ne da wannan, kuma gwani ne akan tsaren Shi. » Don haka burin nan bai halarta a sa shi wai karantawa ba ce. To idan muka fassara shi da buri, to mun fita daga cikin laifi, kuma mun dace da abin da aka fassara ayar. Saboda Annabi (SAW) ya ce, “Biyayya ita ce kyakkyawar dabi’a, laifi kuma shi ne abin da yake yi maka kaikayi a zuciyarka, kuma yake yi maka kokwanto a zuciyarka.” Don haka ne duk wanda ya yi maka fatawa, to ba ya ba ka hujjar da ya dogara a kanta. Allah Ya sa mu dace a kan yardarSa saboda baiwarSa da karanminSa. Ita ma irin kissar Annabi Dauda ne (AS). Malaman Tafsiri sun kuskure wajen fassara wannan aya, «Shin labari masu husuma ya zo maka kuwa? Lokacin da suka dirko ta katanga, sai suka shiga wajen Annabi Dauda, sai ya tsorata da su, suka ce, “Kada ka tsorata da mu, ka yi mana hukunci da gaskiya, ka yi adalci, ka shiryar da mu a kan hanya mikakkiya. Wannan abokina ne, yana da tumaki (99) ni kuma da guda daya tal, sai ya ce in ba shi ita ai tasa ce, kuma ya buwaye ni cikin magana”. Sai Annabi Dauda yace, “Ai ya zalunce ka, a yayin da da ya ce ka ba shi tunkiya guda dayan nan. Sai ya cigaba da cewa, dama haka wasu abokan hulda sashinsu sai su rika zaluntar da shi, sai wadanda suka yi imani kuwa irinsu kadan ne.” Annabi Dauda ya tuno cewa ai wannan hukuncin da ya yi kuskure ne. Sai ya roki Allah gafara, sannan ya fadi yana Sujada ya koma ga Allah.» (Swad : 21-25). Kuma ga mai Tafsirin Zalalul Muhalli, ya yadda da fassara wannan ayar. Ya ce, “Kila an ce, jama’a biyu ne don ya dace da dalilin abin da ya zo na jam’i a cikin lamirin don ya dace da kalmar jam’i daga cikin lamirin. Kuma a wata ruwaya ya ce, «Mutu biyu ne don ya dace da lamirin amma kalmar “Khasmu” ana nufin abokin husuma ne guda daya. Kuma wata ruwaya an ce su wadannan Mala’iku ne suka zo cikin siffar mutane a matsayin masu husuma a tsakaninsu don su nuna wa Annabi Dauda cewa ya yi kuskure, saboda kuskure da ya yi, don an ce shi Annabi Dauda yana da mata (99) ne, kuma akwai wani Sahabinsa yana da mata guda daya, kuma Annabi Dauda yana son wannan matar. Sai ya tura mutumin wajen yaki kuma ya saka shi jagora, wanda a can sai aka kashe shi, sai Annabi Dauda ya auri matar, wai ita ce ta haifa masa Annabi Sulaiman dansa. Kuma sunan mutumin da Annabi Dauda ya auri matarsa shi ne Oriya Ibnu Hannani.” Sai Shaikh Gumi ya ce, “Wannan kissa kamar yadda aka kawo ta, to ba ta dace ba da hankali balle ma a shari’a, da aka aiko Annabi Muhammad (SAW). Kuma mafi yawan mutane da magabata, sun karbe ta, sun kuma gina hukunce-hukunce a kanta.” Yadda kisar take a Tafsirin ayoyin, an kautar da ita daga ma’anarta, kuma an sauya kalmomin, an kuma rikirkita zubin tsarin Al-Kur’ani, an kuma bata kyakkyawar karantarwa mai kima da kuma darasi mai girma, wanda shi ne tsayuwar addinin duniya da lahira. Sai ya ce, “Wata kissa ce don a yi hira da ita, kuma a yi dariya.” Sai Shaikh Gumi ya ci gaba da cewa, “Abin da yake wajibi a ambata shi ne a bar asalinsa yadda Al’Kur’ani ya zo da shi ya zo da shi, don an saukar da shi ne da harshen Larabci, kuma an saukar wa Annabi Muhammad (SAW) da harshensa na Larabci don ya yi wa mutane bayani da abin da aka saukar masa kuma ya yi wa’azi da shi, kuma shi Annabi an saukar masa da harshensa na Larabawa kuma Ummiyi ne shi don ya bayyana wa mutane abin da aka saukar musu kuma su yi aiki da shi da bin umarni.” Zamu ji cigaban wannan bayanin, TUNTUBE DA KURAKURAN WASU MALAMAN TAFSIRI (6), in sha Allah!
Posted on: Sun, 22 Sep 2013 14:14:26 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015