KALUBALE GA YAN SHIAR NIGERIA Daga Umar Malami Sokoto Ashura, - TopicsExpress



          

KALUBALE GA YAN SHIAR NIGERIA Daga Umar Malami Sokoto Ashura, goma ga watan Muharram rana ce da Yan Shiah suke Makokin Husaini (R.A). Kuma Yan Shiah suna ganin wannan rana ta Ashura a matsayin ranar Juyayi da bakin ciki, saboda a ranar ne Hussaini (R.A) ya yi shahada a Karbala. A wannan rana ta Ashura, Yan Shiah na kuka, hargowa, marin fuska, har da tsaga jikinsu da wuqa, aska, barho da takobi, duk saboda juyayin kashe Hussaini a Karbala, kamar yadda kuke gani a wannan hoton na qasa. A Kasashen da addinin Shiah yafi rinjaye, ko yake da adadi mai yawa su sukafi jibintar wannan Commemoration na iskanci da rashin hankali, kamar: - Iran - Iraq - Lebanon - Syria - Bahrain - Azerbaijan - Afghanistan - Turkey - Egypt da sauransu. Kai! Har da kasar India, Pakistan da Indonesia wadanda basu shahara kamar wadancan kasashen ba, ta bangaren addinin Shiah ta fuskar yawa ko kishin Shianci. Amma duk da haka, baa barsu a baya ba, su na gudanarda wannan juyayin na rashin hankali a garuruwa da birane kamar haka: (1). Barabanki - India (2). Tabut - Indonesia (3). Amroha - India (4). Sumatra - Indonesia (5). Hardoi - India (6). Pariaman - Indonesia (7). Karachi - Pakistan (8). Malir - Pakistan (9). Amroha Uttar Pradesh - India (0). Sindh - Pakistan Abin ban mamaki anan shi ne, mi yasa mabiya addinin Shiah a Nigeria, basa irin wannan juyayin, wanda ake tsaga jiki da aska? Shin ko kuna sun ku nuna muna cewa, ku jabun yan Shiah ne, har yanzu baku gama qosawa ba, kuma an bar ku a baya wajen wannan ranar ta juyayi da bakin ciki akan kashe Hussaini (R.A)? Shin ko kuna son ku nuna cewa, wannan Commemoration ba addini ba ne? Hauka ce kawai ta yan Shiah? Kalubale gare ku yan Shiar Zaria, kaduna, Kano, Katsina da sauran yan Shiar Nigeria. Mu dai ta bangarenmu, ina nufin Musulmin gaskiya Annabi ne da kansa ya koya mana cewa muyi azumi ranar tara ga wata da kuma goma ga wata. Don haka wannan shine kadai abin da zamuyi ba zamu kara ba kuma ba zamu rage ba. InshaAllah. Su kuma shi’a ku duba yadda suka musanya Azumi da zubar da jinni. Annabi yace ayi azumi su kuma sunce a’a ba azumi za’ayi ba bakin ciki za’ayi. Allah kayi mana katangar karfe da Shi’anci. Amin
Posted on: Mon, 11 Nov 2013 18:41:06 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015