# KUDIN MARI Wani Bafulatani da Bahaushe suna fada sai Bahaushen - TopicsExpress



          

# KUDIN MARI Wani Bafulatani da Bahaushe suna fada sai Bahaushen ya kwada masa mari. Bafulatani zai rama ke nan sai aka hana shi, ’yan sanda suka kama su.Da suka je ofis Difi’o ya tambaye su yadda aka yi, kowa ya yi bayani. Difi’o ya yanke hukunci, ya ce Bahaushe ya biya Bafulatani Naira dubu biyu diyyar marin da ya yi masa. Bahaushe ya nemi a ba shi lokaci ya je gidaya dauko. Da ya tafi, ana ta jira bai dawo ba, Bafulatani yadade yana jira kuma har ya gaji sai ya daga hannu ya falla wa Difi’o mari, ya ce: “Idan ya kawo dubu biyun sai ka rike!”
Posted on: Tue, 06 Aug 2013 21:14:42 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015