LABARI: Gwamnatin Katsina Za Ta Dakatar Da Biyan Albashin Malaman - TopicsExpress



          

LABARI: Gwamnatin Katsina Za Ta Dakatar Da Biyan Albashin Malaman Jamiar UMYU Gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema, ya yi barazar dakatar da biyan albashin malaman jamiar Umar Musa Yaradua, idan har ba su koma bakin aikin su ba, sakamakon yajin aikin da kungiyar ASUU take ciki. Gwamna Shema ya bayyana hakan a jiya a gidan gwamnatin jihar, lokacin da Sarkin Katsina, ya kai masa ziyarar barka da Sallah. A cewar gwamnan shi lauya ne na kasa da kasa, wanda ya san dokokin aikin gwamnati, saboda haka yana kira da ASUU su gaggauta komawa bakin aikin su, idan ba haka ba kuma gwamnati ba za ta biya su albashi ba. Shin ko kuna ganin daukar irin wannan mataki zai sa kungiyar ASUU ta janye yajin aikin da take yi? 001
Posted on: Fri, 18 Oct 2013 09:41:10 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015