LABARI. KASHI NA 4. KUMA NA ƘARSHE. Cigaba............Ya - TopicsExpress



          

LABARI. KASHI NA 4. KUMA NA ƘARSHE. Cigaba............Ya jimko magani zai barbaɗa sai baƙon nan ya riƙe hannun sa ya ce, Tsaya kawu kada mu yi ɓarna. In dai don ni ne wallahi na yafe. Ka bar su matsuwa ce ta sa su yin hakan. Maigida ya ce, Ai ba don kai ba, idan na kyale gobe ma haka za ta faru. Bari ka gani ko wane kafiri ne yau uwarsa ta rasa shi. Ya yi wuf zai sa magani sai baƙo ya sake riƙe hannunsa ya ce, Tsaya. Gaskiya Yar Allah dai wannan ɗan ƙaramin tari ni na yi shi, amma ban san wanda ya yi biyu ɗin can ba. Maigida ya ce, To in kai ka yi shi mun san lalura ce. Saboda haka bari a zuba kan wanda ba kai ka yi ba. A je a zuba magani sai baƙo ya tare ya ce, Dakata, kai wannan ma ina tsammani ni na yi shi, amma fa na manta ko ni ne ko ba ni ne ba. Maigida ya ce, To tun da ba ka tabbata ba bari a sa kaɗan ƴadda ko wane ne zai wahala kam amma ba zai mutu ba. Maigida ya yi kamar zai zuba sai baƙo ya tare shi ya ce, Tsaya. Don Allah a ɗauka a kan shi ma ni na yi. Amma ka ga wancan, mai yawan can, ba ni na yi shi ba. Maigida ya ce, To shi, ke nan. Tun da ka nuna iya waɗanda ka yi ba kome. Shi kuma mai wancan ya mutu sai wani. Ya matsa kusa da tarin zawon nan mai yawa ya dumbuzo magani zai sa sai baƙo ya cafke hannunsa ya ce, Kai tsaya dai in faɗi gaskiya, ko kuwa? Tun da dai nan gidanmu ne bana wasu ba, ba wani abin ɓoyo. Puhahahahahahahahahahahahahahahahaha. Wayyo ni Allah Faruk cikina yayi ciwo ya ƙulle saboda dariya. Kai! Wai ni Allah!!! Jamaa ku gafar ce ni Dariya ce Wallahi amma zan ɗaura yanzu. Cingaba.....Tun da dai nan nan gidan mu ne ba na wasu ba, ba wani ɓoyo. Puhahahaha wai! Na man ta. Wannan ma ni na yi shi kada a tsaya ana wahala. Sai yaran nan duk suka fashe da dariya maigida ya dubi surukin nan na shi ya ce, Kai wane irin mutum ne da za ka rasa wurin da za ka, ka yi zawo sai gidan surukanka. Ka gan ka dai ba ka gaji kunya ba. Puhahahahahahaha. Wayyo ni kai na, cikina ciwo yake dariya, dariya, dariya. Jamaa dan Allah ku bani mintuna 10 Allah zan iyar muku da labarin nan. Ku yi haƙuri dan Allah Jamaa. Ina zuwa yan zun nan zan ƙara sa Jamaa ku gafar ce ni dan Allah. Faruk Gwandu.
Posted on: Thu, 07 Nov 2013 11:12:44 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015