LABARI: Yau An Bude Filin Jirgin Sama A Jihar Jigawa ….Jirgin - TopicsExpress



          

LABARI: Yau An Bude Filin Jirgin Sama A Jihar Jigawa ….Jirgin Farko Ya Tashi Da Gwamna Sule Lamido Da Tawagarsa Zuwa Kasa Mai Tsarki A yau aka yi bikin bude filin jirgin saman jihar Jigawa dake Dutse, wanda gwamnatin jihar karkashin mulkin Sule Lamido, ta gina. Majiyar #RARIYA ta nakalto cewa jirgin farko da ya fara tashi a sabon filin jirgin a yanzu da misalin 2:00 na rana ya dauki gwamnan jihar, Sule Lamido da ‘yan tawagarsa su 22 zuwa kasar Saudiyya domin sauke farali. An fara gina filin jirgin ne dai a watan Nuwambar shekarar 2012. To yan kano sai kuka mundena zuwa domin tranportation
Posted on: Sat, 05 Oct 2013 14:14:42 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015