Labari mai inganci Wata rana wani mutum yayi mafarki cewa zaki - TopicsExpress



          

Labari mai inganci Wata rana wani mutum yayi mafarki cewa zaki yabiyoshi yana nema ya cinyeshi sai mutumin ya hau wata bishiya zakin ya kwanta a gindin bishiyar yana jiransa,sai mutumin yafara tunanin cewa, yanzu in wannan reshen ya karye yaya kenan? Tunanin hakan yasa yayi maza yaleka kasan reshen sai ya hangi wasu beraye guda biyu da fari da baki suna ta gwaguran reshen har sun kai rabinsa sai ya zabura ya daga kai sama domin ya karyo ganye don ya kori berayen nan guda biyu, yana daga kai ashe akwai zuma tayi ruwa har tana digowa izuwa bakinsa sai ya mance da halin da yake ciki jim kadan sai yaji reshe ya karye da shi yana fadowa yana ihu shi kuma Mr zaki yana jin ihun mutumin sai ya bude baki yana jiran tsammani, sai mutumin ya farka daga barci a firgice, Daga nan sai ya tafi wurin wani malami mai tsoron allah yayi masa bayanin yana son a fassara masa mafarkinsa, sai mal ya tsaya shiru jim kadan sai mal yace, fassarar mafarkinka ba mai wahala bane, da farko dai wannan zaki MUTUWACE kullum take bibiyarka wadan nan beraye kuwa DARE DA RANA kenan suke cinye maka rayuwa shi kuma reshen nan RAYUWARKA kenan ita kuma ruwan zuma DUNIYA kenan, Sabo da haka wa,azine allah (s.w.a) yake yiwa mutane cewa idan mutuwa tayiwa mutane barazana sai kaga suna neman tsira don suna son raywarsu in suka yunkura zasu dauki mataki don gyra ayyukansu sai dadin duniya ta rudesu sai su mance cewa dare da rana suna suna nan suna gurguran rayuwarsu sannu ahankali har sai ajali ya cimmasu sai kaga mutum yana ihu yana neman ceto amma lokaci yariga ya kure Allah ya bamu ikon gyara ayyukan mu kafin lokaci yakure mana.
Posted on: Tue, 03 Dec 2013 10:49:47 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015