MUHIMMANCIN LOKACI......... - TopicsExpress



          

MUHIMMANCIN LOKACI......... BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM Ba wani mutum a duniya da ya kamata ya san muhimmancin lokaci kamar musulmi. Idan musulmi ya wayi gari abu na farko da zai yi shi ne sallar asuba, can bayan rana ta gota ya yi azahar.. haka har wuninsa ya kare yana bibiyar lokuta don ya gana da ubangijinsa. A sati kuma akwai sallar jumu’ah.. a shekara akwai watan azumi, akwai idi, akwai layya, akwai aikin hajji. Idan musulmi yana da jari kuma akwai fitar da zakkah duk shekara. Allah ya rantse mana da lokaci don mu san muhimmancinsa. Lokaci ga dan adam shi ne jarinsa, kai ma dai shi ne rayuwarsa. A cikinsa ne kake murna ko ka samu damuwa. A cikinsa ne kake ciwo ko ka samu lafiya. A cikinsa ne kake talauci ko ka samu arzikin duniya. A cikinsa ne kake shuka alheri ka girbe shi lahira ko ka shuka sharri ka same shi can yana jiran ka gome alkiyama. Don haka a cikin lokacin duniya ne ake samun aljanna ko a fada cikin jahannama. Allah ya kiyaye mu. Lokaci ya fi komi saurin wucewa. Ba ya jira, kuma in ya tafi ba ya dawowa. Sannan kuma Allah bai sanar da kowa lokacin da ya diba ma sa ba. Lokacin da Allah ya ba ka shine tsawon shekarun rayuwarka. Idan ka kwantar da hankalinka sai ka ga dan lokaci ne da ba ya da yawa. Wanda aka ba shi shekaru sittin misali nawa ne za a cire daga ciki na kuruciyarsa? Nawa ne yake kararwa a barci? Nawa ne adadin kwanuka marasa amfani a cikin su? Dan Adam ya kan yi nadama a kan lokacinsa da ya wuce a wurare muhimmai guda biyu: Na farko: Idan mala’ikan mutuwa ya damke shi, ya hakikance cewa tilas zai bar duniya a nan ne yake cewa: Ya ubangiji ku dawo da ni. Domin kila in yi aikin kwarai a cikin abinda na bari. Ina! Wata magana dai ce da shi yake fadar ta, kuma a bayan su akwai rayuwar barzahu da zasu yi har zuwa ranar da za a tashe su. Suratul Muminun: 99-100 Wuri na biyu: Shi ne idan aka yi tashin alkiyama, kowa ya ga sakamakonsa, aka yanke ma kowa hukuncin in da zai zauna. A nan ne dan adam ke cewa: Kuma da zaka ga kangararru sun sunkuyar da kawunansu a wurin ubangijinsu, (suna cewa): “Ya ubangijinmu! Mun fa gani kuma mun jiya, to, ka mayar da mu mu yi aikin kwarai, mu fa tabbas mun gano gaskiya”. Kuma da mun so da mun bai wa kowane mai rai ikon shiriya, amma maganarmu ta riga ta tabbata cewa, lalle sai mun cika wutar jahannama da aljanu da mutane baki daya. To, ku dandani azaba don mantawar da kuka yi da haduwarku ta wannan rana, mu ma mun manta da ku, kuma ku dandani azaba ta din-din-din saboda abinda kuka kasance kuna aikatawa. Suratus Sajdah: 12-14 Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya fada mana cewa, akwai ni’imomi guda biyu da ake kwaruwar dan adam a kan su; lafiya da kuma lokaci. Dalilai uku ne ke sa a kwari mutum game da sha’anin lokaci. Ko dai ya kasance bai yi cikakken amfani da lokacin ba ta hanyar yin abinda ya kamata wanda zai samu babbar lada, ko kuma ya kasa yin aikin lada sam sam, ko kuma a cikin lokacin ya yi aikin zunubi. Mutane sun kasu kashi kashi dangane da lokaci. Wani za ka ga mafi yawan lokacinsa yana cike da abubuwa ne masu amfani, wani kuma duk lokacinsa na sharholiya ne, wani shi kuma bai ma san ya zai yi da lokaci ba! Matsalar wani ita ce bai tsara ma rayuwarsa kome ba, wani kuma bai san muhimmancin lokacin ba. Wani ya sani amma bai da karfin zuciya da kwarin guiwa na maida hankali ga abinda ke amfaninsa. Yana da kyau mu duba rayuwar magabata mu ga yadda suke cin moriyarsa. Abdurrahman bin Mahdi ya bada labarin malaminsa Hammad bin Salamah ya ce, da an ce ma Hammad ga alkiyama nan za ta tsayu bai da yadda zai kara bisa ga aikin da ya ke yi. Ba zamu yi mamakin wannan maganar ba in muka san cewa malam Hammad ya rasu yana cikin sallah. Saurari wani dalibin ilimi abinda Abu Hatim Ar-Razi Rahimahullah abinda yake cewa: “Mun nemi malam Ka’anabi ya karantar da mu Muwadda sai ya ce to ku zo da safe. Sai muka ce masa da mun yi asuba wurin malam Hajjaj muke zuwa. Ya ce, to ku zo in kun kare. Muka ce sannan muke zuwa wurin malam Muslim bin Ibrahim. Ya ce to ku zo in kun gama. Muka ce ko da muke gamawa azahar ta yi, sannan muke karatu ga Abu Huzaifa. Ya ce, to, ku zo bayan la’asar. Muka ce, makarantar Arim. Ya ce to ku zo bayan magariba. To, daga nan muka rinka zuwa wurin sa idan an yi magariba sai ya fito ana sanyi ya nadiye kansa ya yi ta karantar da mu har illa mashaAllahu”. Ta hanyar amfani da lokaci ne kawai ake iya fito da baiwa iri iri da Allah ya yi wa dan adam. Bincike ya nuna cewa akasarin mutane ba su amfani da kashi 25 cikin 100 na baiwar da Allah ya ba su. Yaron da ya fadi jarabawa kuma ya rufe aji yana iya zama na daya ba a makarantarsu kawai ba a fadin jiha gaba daya inda an yi kokarin fitowa da baiwar da Allah ya ba shi. Shiriritaccen da zaka gan shi yana kashe wando a bakin titi yana iya zama babban malami ko babban mawallafi ko kwararren likita ko gogaggen dan siyasa ko fitaccen dan kasuwa. Amma an watsar da baiwar da Allah ya ba shi, shi ya sa ya lalace. Wanda ya zo na baya a wajen tsera ko gasar karatun alkur’ani yana iya zarce kowa in da an tona baiwar Allah da ke tattare a cikin sa. Kana iya gwada wannan ga dan takara a wajen tserar gudu idan ya kasa, ya koma baya har ya kai ga faduwa saboda gajiya. Idan likitoci suka auna shi a lokacin zasu ce mana akwai sauran karfi da kuzari mai yawa a jikinsa amma yana bukatar abinda zai zakulo wannan karfin. Ya zamu gane wannan? Mu sakar masa zaki ko maciji misali. A nan ne zaka sha mamaki. Suna yin arba da zaki zaka ga ya tashi ya ruga da gudu, irin gudun da can da farko ma bai yi shi ba. Me ya tono wannan kuzari na gudu daga jikinsa? Daga sama aka sauko masa da shi? A’a. Daman yana nan cikin jikinsa amma yana neman abinda zai motsa shi! Wannan shi zai fassara maka irin albarkar rayuwar magabata wajen jihadi da karantarwa da rubuce rubuce da makamantansu. Sun sanya wata manufa a gaban su ita ce neman yardar Allah. Wannan manufa sai take fitar da iyakar abinda yake yiwuwa na baiwar Allah da ke cikin su. In ba don Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ba da su sayyidina Umar da Ibnu Mas’ud da Khalid bin Walid da sauransu duk iyakar su su zamo makiyaya ko ‘yan kasuwa ko ‘yan tauri ko wani abu mai kama da wannan. Amma da aka samu jagora cikakke mai manufa sai ya fito da ikon Allah a cikin su. Nan take kowanensu ya taka rawa mai muhimmanci a tarihin duniya. Wani daga cikin magabata ke cewa, wani lokaci sai bacci ya fara dauka ta, ina cikin jin dadinsa sai in tuna da wuta da aljanna. Idan na tuna haka sai in ga na zabura kamar zaki na tafi zuwa kiyamullaili. Ko kun ga yadda tsayayyar manufa take sa a kula da muhimmancin lokaci? Fetur idan aka zubar da shi ga kasa sai kasa ta shanye shi bai amfani kowa ba. Amma in da an zuba shi a mota fa? Wannan shi ne misalin hikimomin Allah da bamu yi amfani da lokaci muka ci moriyar su ba. Wannan kuma shi ne sirrin da ya sa idan an yi yaki musulmi ke galaba a kan kafirai. Allah Ta’ala ya ce: Kuma kada ku yi rauni wajen yakar mutanen, in har kuna jin radadi, to hakika su ma suna jin radadi kamar yadda kuke ji, kuma kuna fatar samun abinda ba su fatar samun sa daga wurin Allah. Kuma Allah ya kasance mai cikakken sani, mai cikakkiyar hikima. Suratun Nisa’i: 104 A wata ayar kuma Allah ya ce: Kuma kada ku yi rauni, kada ku yi bakin ciki, domin ku ne madaukaka in har kun kasance muminai. Suratu Ali Imran: 139 Wani malami ya tsaya a gaban ‘yan wasa suna ta sharholiyarsu. Sai aka gan shi yana jin haushi yana ciza yatsa. Don me? Ya ce, wallahi na so a ce lokaci kaya ne, sai in sayi na wadannan don ba ya da amfani gare su. Ya ku bayin Allah! Ga wasu muhimman shawarwari da zasu taimaka mana wajen kula da lokaci: 1. Kada ka yarda ka bar wani lokaci ‘yamti, domin wannan ba dabi’ar mumini ba ce. Allah Ta’ala ya ce: “Idan ka gama al’amurran duniya, to ka kafu wajen ibada. Kuma ka yi kwadayi zuwa ga ubangijinka” Suratus Sharh: 7 -8 Da zaran ka samu lokacin da ba komai da zaka yi, samar masa wani abinda zai amfane ka. Misali lokacin jiran wani, kamar jiran likita a asibiti, ko layin shiga mota, ko kuma kan hanya daga wani gari zuwa wani gari ko wata unguwa zuwa wata unguwa. A lokacin da kake tuka babur ko aka dauka a kansa zuwa kasuwa. A lokacin da kake shago amma ba wani abokin ciniki tare da kai. A duk irin wadannan lokuta kana iya kago wani abu da zai amfane ka kamar yin zikiri ko karanta wani littafi ko kuma wata tattaunawa mai muhimmanci da wani wanda kake tare da shi. Da wannan ma’aikaci na iya cin moriyar abinda ya yi rara na lokacinsa. Dan kasuwa ma haka. Mai achaba da mai lodi da kafinta da mai kasa kaya a titi duk suna iya amfani da lokutan rara a wajen ambaton Allah da makamantansa. Ibnu Taimiyyah Abdussalam yakan ce ma dansa Ibnu Taimiyyah Ahmad: “Zo ka yi karatu kusan da ban-daki kafin na fito” don ya saurari karatu a yayin da yake biyan bukata, gudun kada lokacinsa ya tafi a banza a daidai wannan lokaci. 2. Yi kokari a kullum ka gabatar da abinda ya fi muhimmanci. Idan ayyuka biyu suka hadu babba da karami ka fara gabatar da babba. Idan kuma dayansu yana amfaninka ne kai kadai dayan kuma yana amfanin jama’a, fara yin mai amfanin jama’a tukuna. Kamar sallar nafila da karantar da mutane. Idan kuma aiki daya yana da lokaci mai wucewa dayan kuma ana iya yin sa a koyaushe to, fara gabatar da wanda lokacinsa ke wucewa. Kamar addua a lokacin ijaba. 3. Ka auna duk maganar da zaka yi don ka tantance amfaninta ko cutarwarta. Idan ka yarda ba ta da amfani sai ka bar ta ka yi wata ko kayi shiru don ka tsira da lokacinka. 4. Yi kokari ka gano lokutan da kake tozartawa a wuni. Misali, daga sallar asuba zuwa karfe goma, awa ne? Wane amfani suke maka? Kar ka manta cewa, kafin wannan lokaci ka share dare watakila kana barci. Tsakanin magariba da isha’i me kake yi? Daga isha’i zuwa shiga bacci fa? Idan ka gano wadannan lokutan sai ka tsara yadda za ka rage tozarta su. 5. kada ka bari mutane su rika sitarin lokacinka. Duba misali yadda Imamul Bukhari yake yi idan ya yi bako mai nauyi. Abinda yake yi shi ne sai ya dauko littafinsa ya ce ma bakon yana da kyau mu karanta wannan domin mu amfana. Shi kuma Ibnu Akil Al-Hambali idan ya yi irin wadannan baki sai ya dauko alkalumansa na rubutu ya ce su taya shi fekewa. 6. Tuna mutuwa na taimaka maka ainun wajen kula da lokacinka. Duk matafiyi idan ya ci rabin hanya zai ji cewa ya kusa kai. Amma a mas’alar rayuwa da mutuwa ba mu tuna haka. Sai ka ga mutum in ya yi shekaru talatin yana ganin tukuna bai yi kome ba. Shi ya sa ake cewa mafi yawan mutane suna mutuwa ne a cikin kuruciya, don ba a dauka sun kai lokacin mutuwa ba. Rayuwar dan adam ba ta da tsawo. Akwai halittu na daji da ke kai shekaru 200 zuwa 300 ko abinda ya fi haka. A bishiyoyi ma akwai wadanda su ke kunne ya girmi kaka. Su duwatsu ba a ma maganar su. Don haka babu mamaki ka ga shekarunka sun kare nan take. Samu wata rana ko da a cikin wata ne ka je ziyara makabarta kai kadai ka tsaya ka kalli wadanda ke kwance. Ka tambaye su, mene ne gurinku? Me kuke fata a yau? Ba zasu ba ka amsa ba. Amma ka sani da zasu buda baki da zasu ce, muna son mu dawo duniya mu ci ribar lokaci. 7. Sanin cewa bayan mutuwa akwai tambaya. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya ce: “Ba wanda zai daga kafarsa a ranar alkiyama har sai ya amsa tambayoyi guda hudu: Ta farko: Rayuwarsa a ina ya karar da ita? Ta biyu: Kuruciyarsa a kan me ya tafi da ita? Ta uku: Abinda ya sani ko ya yi aiki da shi? Ta hudu: Dukiyar da ya samu a duniya, ta ina ya same ta kuma ta yaya ya kashe ta? Ya ku ‘yan uwa musulmi! Muna gaf da shiga wani wata mai albarka wanda masu dabara suke cin kasuwar lahira a cikinsa. Watan Ramadhan wanda ayyukan lada suka fi komi kadari a cikinsa. Watan da ke da Lailatul kadari a cikinsa. Wane irin shiri muka yi domin tarbonsa? Wace ajenda muka sanya ma kanmu don ganin mun amfana da shi watakila shi ne na karshen da wasunmu zasu gani? Wasu an yi na bara da su amma ba za ayi na bana da su ba. Wasu ma daga cikinsu yanzu an rabe dukiyoyinsu, an aure matayensu, an rufe shafin tuna su. Suna can a tsakanin ayyukansu da suka shuka a nan duniya... Allah Kabamu Ikon yin amfani da lokacinmu..... Allahumma-Ameeeen
Posted on: Thu, 03 Oct 2013 07:33:55 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015