MUNA MUTUQAR BUKATAR - TopicsExpress



          

MUNA MUTUQAR BUKATAR ADDUA!!! ******************************* Assalamu Alaikum mallam Ina buqatar addua malam domin mahaifina tun da ya fita ranar asabar har yanzu babu wani labari akansa, kuma duk inda muke tunanin zamu sameshi babu wani alama, dan Allah malam a taimaka Allah ya bayyana mana shi. Wassalam (Daga Uqbatu Maisarah) AMSA ****** Innalillahi wa inna ilaihi Rajiun!!!!! Lallai dole hankalinku ya tashi. Musamman ma idan akayi laakari da yanayin zamanin nan namu. Shawarata anan, ku yawaita faddin LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAHIL ALIYYIL AZEEM Insha Allahu Allah zai fito muku dashi. Koda yana hannun mugaye, insha Allahu ba zasu samu wata dama akansa ba. Allah zai kiyayeshi. Manzon Allah (saww) ya taba gaya ma wani sahabinsa irin wannan adduar yace masa yayita. Alokacin da kafurai suka sace masa yaronsa. Mutumin yayi adduar kuma Allah ya fito masa da yaronsa cikin sauki. Kuma ina rokon yan uwa cewar DON ALLAH mu taimaka ma wannan bawan Allah da addua. Muma Allah zai taimakemu. Allah ya sawwake. Allah yasa adace.
Posted on: Thu, 07 Nov 2013 10:58:11 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015