MUTUWA DAI KOFA CE! KUMA KOWA SAI YA SHIGE TA!!! Yaa Kai Dan - TopicsExpress



          

MUTUWA DAI KOFA CE! KUMA KOWA SAI YA SHIGE TA!!! Yaa Kai Dan Adam: Ka riski rayuwarka kafin gushewarta. Ka riski furen samartakarka kafin ya kakkabe. Ka riski danyar lafiyarka kafin ta bushe. Sannan ka tuna cewa lokacinka a rayuwa shi ne mafi tsadar abinda ka mallaka cikin rayuwarka, tahanyar zance na kwarai da aiki na gari. Kuma ka sanya darenka da ranarka tamkar wata gonace wacce kake shuka biyayyarka ga Allah da ayyukan alkhairi… Kumaka yi gaggawa wajan tuba daga dukkanin zunubinda ka aikata komai qanqantar shi ko kuma girman shi. Domin kuwa mafi muhimmancin kofa da aka budeta saboda mu itace KOFAR TUBA! Kuma zaa rufeta lokacinda rayukanmu suke fita daga jikkunan mu. Ita kuma mutuwar bata da lokaci balle dan sako! Bata da alama balle amata shiri! Bata san dan gida ba balle bako! Ba ruwanta da yaro balle babba! Bata tausayin mara lafiya balle mai lafiya! Bata san mawadaci ba balle talaka! Hmmmmmmm! *Ajiyar zuciya* Mai hankali dai shi ne wanda ya waazantu daga wanin sa. MUTUWA DAI KOFA CE! KUMA KOWA SAI YA SHIGE TA! AMMA BABBAR DAMUWAR ITA CE: MEYE ZAI KASANCE BAYAN MUTUWAR ?? HUTU NE KO RASHIN SA? Mutum zai kasance cikin kwanciyar hankali da walwala A BAKUNTARSHI TA DUNIYA matukar yana da zuciya mai masa waazi fa fadakar da shi Ya Allah mai jujjuya zukata,ka tabbatarda zukatunmu bisa biyayya gareka! Jummaa mufeedah
Posted on: Thu, 07 Nov 2013 18:16:30 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015