Manyan malaman kasar kenan a lokacinda sukayiwa - TopicsExpress



          

Manyan malaman kasar kenan a lokacinda sukayiwa Najeriya addu’a a filin Arfa, Saudiyya. Wadanda suka jagoranci addu’ar sun hada da Shugaban Jibwis na kasa Ash- Sheikh Abdullahi Bala Lau, Sheikh Yakubu Musa Hassan, Sheikh Sa’idu Hassan Jingir, Sheikh Dk. Alhassan Sa’eed Adam, Sheikh Dk. Aminuddeen Abubakar, Sheikh Dk. Mansur Sakkwato, Sheikh Tijjani Bala Kalarawi, Sheikh Aliyu Sa’id Gamawa da Sheikh Dahiru Usman Bauchi. An yi taron addu’ar da manyan malamai daga kasashen Yarabawa da Inyamurai. Shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya Aminu Waziri Tambuwal (na farko daga dama) da sanatoci da ’yan majalisu da sauran ’yan Najeriya ne suka halarci taron wanda Amirul Hajji na kasa Shehun Borno Mustafa Garbai Elkanemi ya jagoranta HADIN KAN MALAMAN NAJERIYA A MAKKAH YAUDARA CE KAWAI - SHEIKH DAHIRU BAUCHI Category: Manyan Labarai Published on Friday, 01 November 2013 00:00 Written by Mu’azu Hardawa, Bauchi Hits: 563 An yi ta yunkurin ganin an hada kan musulmin Nijeriya. A bana ma malaman sun hadu a filin Arfa a kasar Saudiyya, amma Sheikh dahiru Usman Bauchi da ya dawo ya bayyana wa wakilinmu cewa duk wani batun hadin kan musulmi a Nijeriya yaudara ce kawai don haka ya kamata a fuskanci gaskiya don a gudu tare a tsira tare. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: Akaramakallah me za ka ce game da yadda aikin Hajjin bana? Sheikh: Dukkan musulmi muna yi wa juna murnar gama wannan rukuni na aikin Hajji. Kuma akwai wadansu abubuwa da ke faruwa inda wadansu suka mayar da mutane kamar wawaye ko mahaukata. Kowa ya tabbata babu wanda ke zuwa Makka da Madina sai musulmi, mushrikai ba sa zuwa ta wajen shari’a ko doka. Amma abin da ke damunmu ana ta kokarin gyara matsalar rashin fahimtar juna kuma kowa ya aminta da yin hakan, amma har yanzu ‘yan izala suna gudunmu ba sa zuwa masallatanmu kuma ba su daina wa’azin da suke kafirta mu da cewa mu mushrikai ne ba, ba sa binmu sallah, ba sa cin yankanmu, alhali mu dukkan maganar sulhu da ake yi mun sakankance kan batun gaskiya ne. Amma abin mamaki wadansu daga cikinsu ana tufka suna warwarewa, suna farfagandar suna cewa kar a bi mu sallah, kar a ci yankanmu, har yanzu kuma daga cikin manyansu muna gani babu wani mai tsawata musu don su sassauta ra’ayinsu saboda mu hada kai mu gudu tare mu tsira tare a wannan lokaci da ake bukatar hadin kan musulmi. Saboda mun san mawuyacin halin da muke ciki idan su ba su sani ba. Tunda ba su fasa kafirta mu da aibanta mu ba, shi ya sa muke ganin son siyasa ne ke sa idan sun je Makka sai a kira mu a tara mu waje guda a ce mu yi addu’a su kuma mika mana hannu mu gaisa, to me ya kawo mushriki Makka da Madina har za a gaisa da shi? sannan kuma sai su dawo su sake cewa an hada kai, a ina aka hada kai? mu dai har abada ba za mu hada kai da mai kafirta mu ba yana zagin Shehu Tijjani da Sidi Abdulkadiri da sauran waliyai ba, sai ya daina. Don haka nake mana nasiha gaba daya don kar mu yi wasa da hankalin mabiyanmu,bu saboda mu ba yara ba ne, addinin musulunci kuma ba wasa a cikinsa ko yaudara, shi ya sa ni ba zan iya shiru mu tafi kan kuskure ba, don haka kullum nake fita fili in fadi abin da ke damunmu da kowane mutum ba tare da shakka ko tsoro ba, don mu samu mafita kowa ya gyara kurensa ya kasance an bi shari’a yadda ya kamata, kar mu zama masu wasa da hankalin mabiyanmu, saboda kowa daga gare mu yake koyi. Hakan ya sa idan muka yi kuskure ko aka yi mana gurguwar fahimta mukan fi kowa samun matsala. Idan ba za su daina aibanta mu ba, babu ruwanmu da su, sai mu ci gaba da tafiya irin wacce ake yi ta zaman doya da manja, amma idan an gyara mun fi kowa farin ciki a tafi kan igiyar Allah ba tare da rarraba ba. Ina tsammani kun ji labari da azumi manyan Kiristoci sun karramamu sun zo har gidajenmu a nan Nijeriya mun sha ruwa tare, yin haka ya sa mun zama kirista ko sun zama musulmi? ba daya, amma ka ga wannan ya nuna akwai girmamawa da nuna zaman lafiya, ba gaba, akwai yarda a tsakani. Saboda Kirista ba ya zuwa coci yana aibantamu yana zagin Shehunanmu ko ya kafirta musulmi ta hanyar daura lasifika yana yawo yana cin mutuncinmu da shehunanmu. Karramamu da suka yi ta hanyar zuwa gidajenmu a sha ruwa ya kauda duk wani tunani na zahiri game da rashin yarda da juna. Ba haka yake aukuwa tsakaninmu da ‘yan Izala ba, saboda ko a Makkan idan sun ganmu ba sa yi mana ganin musulmi, don Allah wannan ba zai bata mana rai ba? Sun san haka, mun san haka, amma mu ba za mu ci gaba da rikewa a zuciya ba shi ya sa nake fita fili nake bayyanawa don mu taru mu gyara mu daina yaudarar mabiyanmu. Sun sani, mun sani,
Posted on: Fri, 01 Nov 2013 10:34:19 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015