***Mu Dau Darasi*** Wata rana anyi wani kwararren - TopicsExpress



          

***Mu Dau Darasi*** Wata rana anyi wani kwararren magini(builder) wanda shekarunsa ya ja sosai,tsufa ya fara kamashi,sai yace gara dai ya bar wannan aiki na gini ya huta a gida. Ya gayawa ubangidanshi akan yana so yayi ritaya,saboda ya huta kuma ya kasance tare da iyalansa,yace ya san dai idan ya bar aikin ba zai dinga samun albashi ba,amma barin aikin nashi yafi.. Sai ubangidan ya tausaya masa,kasancewar yasan tunda ya fara aikin ma bai gina gida na kanshi ba,sanna kowa yana yabon aikin wannan tsoho,yasan zai rasa kwararren maaikaci. Sai yace wa wannan mutumin,ina so kayi min abu daya kafin kayi ritaya. Ka gina min gida,wanda zai zama shine aikinka na karshe kenan. Sai mutumin yace ya yadda da wannan batu na ubangidanshi. Kasancewar wannan magini ya sa ranshi akan riyata,koda ya fara aikin gina wannan gida sai ya nuna halin ko-in-kula,ya saya kayan ginin mai arha,sannan yaki bada hankali sosai akan aikin ginin kamar yadda ya saba,a takaice,yayi ginin da babu kargo,sam ginin kamar ba shi yayi ba.. Da ya gama aikin ginin,sai ya qira ubangidanshi ya nuna mishi komai. Sai ubangidan ya dauko wasu takardu da kuma makullin wannan gida yace Ga wannan gida na baka,kyauta ce daga wajena,kasancewar naji dadin aiki da kai.. Wannan mutumi a take yaji kunya ya kamashi,takaici ya lullubeshi. Yana mai cewa,da nasan wannan gini wa kaina zanyi,da na kera ginin da ban taba irinshi ba wajen kyau.... To jamaa,muma namu rayuwar kamar dai na wannan magini ne. Allahu Azza Wa Jallah ya kawo mu duniya ba don komai ba sai don mu gina gidajenmu a cikin Aljannah da kyawawan aiyyuka. Saboda haka,sai mu san wani irin gini zamuyi anan Duniya domin kasancewa a cikinta a rayuwar gaskiya.. Allah Ya sa mu dace baki daya,amin. Adama SB Adm 007
Posted on: Sat, 09 Nov 2013 12:20:29 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015