Salam Jamaa ina muku barka da warhaka ya mukaji da harkokin yau da - TopicsExpress



          

Salam Jamaa ina muku barka da warhaka ya mukaji da harkokin yau da kullum. Allah ya taimake mu. Ameen. Sau da yawa na kanji mutane da yawa ta wannan kafa suna yawan kira da fatan Allah ya kawo mana canji da shugabanni masu adalci da kishin kasa da rikon Amana, abin tambaya anan shi wai mu talakawa mun shirya fatan samun wannan canji? Domin in kasami shugaba jagora lalatacce to mabiya talakawa su ma haka suke, kamar yadda in ka sami shugaba jagora Adali to haka talakawa suma Adalai ne mutanen kirki. Amma na tabbata muna da karancin Adalci da yiwa juna uzuri a tsakanin mu. Da farko dai mun iya zagi da cin mutuncin shugabannin mu da malaman mu, alhali mu a junan mu talakawa ba mu kyautatawa da yin Adalci a junan mu sai zagi da kazafi da munafunci da zato da cin naman junan mu da Annamimanci da cin Amana da hassad da ganin kyashi. Duk wadan nan abubuwa ne da suke faruwa a tsakanin mu, mu talakawa mabiya, domin Allah yace idan Alumma ta sami shugabannin Adalai mutanen kirki to daga gare ni ne, idan kuwa kuka sami shugabanni Azzalumai, fajirai, fasikai maciya Amana to daga gareku ne, ashe da wannan zamu gane cewa mu kanmu talakawa akwai alamomim tambaya a kan mu. Don haka wallahi Allah matukar muna bukatar Shugabanni adalai masu rikon Amana da kishin kasa ya zama wajibi mu talakawa mu gyara halayen mu, in mu kai haka to da yardan Allah zamu cimma burin mu.
Posted on: Tue, 26 Nov 2013 04:09:55 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015