TAFIYAN SHIRKA A CIKIN MUSULMAI TAFI BUYA FIYE DA TAFIYAR - TopicsExpress



          

TAFIYAN SHIRKA A CIKIN MUSULMAI TAFI BUYA FIYE DA TAFIYAR TURURUWA INJI MANZON ALLAH (S.A.W) Hadisi ya Inganta yana cikin Sahihul Jami hadisi na 3731 kuma yana Sahihul Adabil Mufrad littafin Al- Imamu Bukhari hadisi na 716. Maakilu bn yasar yana cikin sahabban Manzon Allah (S.A.W) yace wata rana nida Sayyidina Abubakar muka tafi wajen Annabi (S.A.W) da muka zo wurin shi sai yace Ya kai Abubakar! Lallai shirka acikin ku musulmai buyanta yafi na rarrafen tururuwa, Abinda Annabi yake nufi shine yadda baka iya jin tafiyar tururuwa hakanan baka iya jin tafiyar shirka a cikin musulmai, jamaa hatsarin shirka yana da yawa, Sai sayyidina Abubakar yace ya Rasulullah! ashe akwai wani abu da ake cema shirka sabanin sanya ma Allah abokin tarayya? Sai Annabi yace Na rantse muku da wanda raina ke hannunsa lallai shirka tafi buya fiye da rarrafen tururuwa, wato yana kara karfafa masa, Sai Manzon Allah yace masa kana so in nuna maka wani abu wanda inka fadi abinnan Allah zai kawar maka da shirka mai yawa da kuma kadan? Sai Annabi yace masa kace ALLAHUMMA INNI AUZU BIKA ANNUSHRIKA BIKA WA ANA AALAM WA ASTAGFIRUKA LIMALA AALAM, Maana Ya Allah ina neman tsarin ka kada inyi tarayya da wani dakai ina sane kuma ina neman gafarar ka da shirka da nayi alhali ban sani ba. Kunga Ashe mutum yakan yi shirka da Allah a cikin rashin sani, kuma yakan yi shirka da Allah da gangar. Annabi yace ma Sayyidina Abubakar idan ka rike wannan adduar to Allah zai rabaka da shirka komin kankantarta. Mutumin da yakeso ya samu addua wadda zata taimaka masa Ikhlasi ka sami tsarkakan zuciya abinda zaka rinka yi kayi shi don Allah to sai ka rike wannan addua na Annabin mu Muhammad (S.A.W). Don haka muyi hattara da gwama Allah da wani a wurin bauta masa, muyi aiki yadda Annabi (S.A.W) ya koyar damu. JUMU@ MUBARAK.
Posted on: Thu, 07 Nov 2013 21:04:18 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015