**TAUHIDI** Assalamu alaikum, Yan uwa barkanmu da sake saduwa a - TopicsExpress



          

**TAUHIDI** Assalamu alaikum, Yan uwa barkanmu da sake saduwa a wannan Littafi na Haqiqatu-tauhid, wanda Sheikh Muhammad Hassaan ya Rubuta, Idan bazaku manceba, muna cikin bayanine akan Dagutai, muka tsaya kan shuwagabannin Dagutu, Yau zamu kawosu da ikon Allah: SHUWAGABANNIN DAGUTAI GUDA BIYAR: 1, SHAIDAN wanda ke kira ga bautawa wanin Allah, dalili shine fadin Allah s.w.a: ((Ashe bamu dauki Alqawarinku ba ya Yan-Adam akan kada ku bautawa shedan, Lallai shi maqiyine a gareku mai baiyananniyar qiyayya a gareku)) -Yaasin: 60-. 2, JAIRIN SHUGABA wanda ke juya hukuncin Allah madaukaki, dalili shine fadin Allah taalaa: ((Ashe bakuganiba zuwaga wadanda ke tsammanin su sunyi Imanida abinda aka saukar agareka (Manzon Allah) da wanda aka saukar a gabaninka ba, suna son kai hukuncinsu zuwa ga Dagutu, kuma haqiqa an Umarcesu da su bijire masa, shikuma shaidan yanaso ya batar dasu bata mai nisa)) -Nisaai 60-. 3, WANDA KE HUKUNCI DA WANIN ABINDA ALLAH YA SAUKAR ( da wanin Qurani da Hadisi), dalili shine fadin Allah Madaukaki: (Duk wanda baiyi hukunci da Abinda Allah ya saukarba, to tabbas wadannan sune kafirai)) -Almaaedah:44-. 4, WANDA KE TSAMMANIN SANIN GAIBU ga wanin Allah, tunda babu wanda yasan Gaibu baicin Allah madaukaki, dalili shine Fadin Jallah: ((Masanin gaibu, baya baiyanar da gaibinsa ga kowa * sai dai wanda ya amince dashi daga Manzanni, to sai ya saukar da tsaro (malaiku)a gabansa da bayansa)) -Jinn: 26-27-. Da kuma fadin Allah: ((Kuma a wajensa Mabudan Gaibu suke, babu wanda yasansu face shi, kuma yasan abindake kan tudu da wanda ke ruwa, kuma babu abinda ke fadowa na daga ganye face ya san dashi, ko wani tsuro a cikin duhun qasa ko wani danyen abu, ko busasshe face yana acikin littafi baiyananne)) -Anaam:59-. A darasin gaba zan kawo mabudan Gaibu guda 5, da kuma cikon Shugaban daguta na biyar din. Allah ya tsare mana imaninmu.
Posted on: Mon, 25 Nov 2013 12:49:59 +0000

Trending Topics



ess.com/Good-morning-dear-friends-and-another-good-day-it-is-Just-came-topic-257143297792917">Good morning dear friends, and another good day it is! Just came

Recently Viewed Topics




© 2015