WAIWAYE: Yadda aka gudanar da maulidin Sayyida Fatima (AS) na - TopicsExpress



          

WAIWAYE: Yadda aka gudanar da maulidin Sayyida Fatima (AS) na Halkoki a Kano Daga Bilkisu Yusuf Maitaya Kano 08069162021 A wannan shekara ta 1434 (2013), maulidin Halkoki da yankuna (Zones) a Kano ya sauya sabon tsari, saboda Malam Muhammad Turi ya hada zumunci tsakanin yankunan da Halkoki. 1- Halkar Rasulul Akram (Kurna) da Yankin Tudun wada. 2- Halkar Amirul Mumineen (Na’ibawa) da Yankin Kura. 3- Halkar Sayyida Zahrah (Gwammaja) da yankin Kazaure. 4- Halkar Imam Hasan Almujtaba (Sabon Titi) da yankin Malam Madori. 5- Halkar Imam Husain (Tudun wada) da yankin Birnin Kudu. 6- Halkar Imam Aliy Zainul Abidin (Fagge) da yankin Durbunde. 7- Halkar Imam Bakir (Kawo) da yankin Gumel. 8- Halkar Imam Ja’afar Assadik (K/Waika) da yankin Gwarzo. An fara Maulidin a Halkar Kawo ranar Talata 6/6/1434 (16/4/2013). Sun yi gayyato mata Kiristoci na Zumunta Group daga Cocin ECWA, sun kuma sami halarta. Malama Maimuna Abdullahi ta yi bayani kan Sayyida Zahra (SA) da muhimmancin hadin kai tsakanin Musulmi, inda ta yi nuni da fakewa da ake yi da Boko-Haram wajen dasa bama-bamai a masallatai da Coci. Ta ce makida ce ta makiya don a hada al’umma fada. Sun yi gonar Fadak, sun zuba kayan marmari, har da wainar kwai wadda ake soya ta a Tanda, wadda mutanen Nijar suka fi yin amfani da ita, aka kulle ta a leda, suka sa a Fadak. Malama Maimuna da Matan Zumunta Group ne suka shiga cikin Fadak suka dibi abin da suke bukata daga arzikin Sayyida Zahrah. Sun ba wa Marayu katan din Taliya 5, katan din Omo 2, na sabulun wanki 1, na wanka 1, Man Shafawa katan 1, Set din kayan Yara dozin 3; sun kai wa Maguzawa a kauyen Gwarzo. Ranar Laraba 7/6/1434 (17/4/2013) an yi a Halkar Na’ibawa. Sun yi Maulidin a Sallari. Malaman Wahdan da suka sami halartar Maulidin sune: Malama Huwaila, Malama Habiba M. Habiba, Malama Basira da Malama Khadijah Yunusa daga Ummun Nabiyy Islamiyyah. Sun yi bayanai daban-daban, wadanda suka shafi Tarbiyyar Yara, Gyara Zamantakewa na Aure, dss. Malama Maimuna Abdullahi ta yi bayani a kan Sayyida Zahra (SA). Maulidin ya sami halartar jama’a da yawa, musamman ’yan uwa na yankin Kura. Sun nuna musu zumunci, inda suka zo da yawa da ’yan Fudiyyarsu, wadanda suka kawata wajen da yin fareti. Sun bai wa iyayen Marayu tallafi na Semovita 4, Taliya Selva katan 8. Sun kai tallafin Roba Dozin 3, Takalma Dozin 3, Alli (Chalks) Kwali 2, Klin katan 1 Gidan marayu. Su ma sun yi Fadak da Fadar Sayyida. Sun kawata wajen da wata karagar Sayyida ta musamman, hade da kayan marmari. Ranar Alhamis 8/6/1434 (18/4/2013) an yi Maulidin a Halkar Gwammaja. Sun yi a Gwammaja layin ’Yan Carkwai. Malamar Wahda, Malama Amina ta yi takaitaccen bayani a kan Sayyida Zahra. Daga nan sai Malama Maimuna Abdullahi ta yi bayani a kan falalar wanda ya raya Sha’a’irillahi yana da lada mai yawa. Imam Sadik ya ce, “ku raya al’amarinmu. Allah ya ji kan wanda ya raya al’amarinmu.” Sun bai wa Makafi da Kutare da Guragu kyauta. Sun shirya Tamsiliyya a kan mutane su san su waye Ahlulbaiti? Ranar Juma’a 9/6/1434 (19/4/2013 an yi Maulidin a Halkar Sabon Titi a Gadon Kaya, kofar Gidan Shahid Muhammad Aley. Sun gabatar da kirari ga Sayyida da Tamsiliyya kan muhimmancin ba da Hakkin Shuhada. Sun gabatar da wasu Yara Mata ’yan biyu, kamar su daya suka yi gaisuwa ga Sayyida da Turanci. Wasu Yara Mata Fulani sun yi gaisuwa ga Sayyida da Fulatanci. Sun yi Tamsiliyyah kan Matsalolin Aure, musamman auren Hausawa, kan cewa tsakanin Maza da Mata su waye suka fi hakuri? Sun yi Musabaka tsakanin Makarantun Islamiyya na Matan Aure: 1- Jami’atu Sayyida Hafsa Kwalwa, da 2- Ummil Muminina A’isha. Sun yi Fadak, suka kawata ta da Fulawowi da Tuffah, Inabi, Kwai, dss. Malaman Wahda, kamar su Malama Ummal Khair Abdulyassar, Malama Husaina Uba, Malama Sa’a datu Abubakar sun yi jawabi. A jawabinta Malama Ummal Khair a kan sirrin hadin kan Musulmi, ta ce babu ci gaba wajen aibata juna da wargajewar Musulmi. Malaman da suke aibatawa da kafirta juna suna tafka babban kuskure. Me ya sa mu’amala da juna yake zama hadari, alhali muna tare a Jami’o’i da manyan Makarantu? Malama Husaina Uba, a nata jawabin a kan Tarbiyyar Yara, ta ce Tarbiyya hakki ne a kan Iyaye, su ba wa ’ya’yansu tun suna ciki har su zo duniya. Uwa ita ce Malamar farko ga ’ya’yanta. Yana da kyau a nuna wa Yaro son Allah da jin tsoran sa wajen kiyaye dokokinsa. A dinga nuna masa ayyukan alkhairi tun yana karami. A dinga tambayar sa kan burinsa a gaba don a ji dadin saita shi. A karshe ta gargadi Iyaye Mata kan muhimmancin jan yaro a jiki, musamman ’Ya da take da matukar bukatar kulawa. Malama Sa’adatu, a nata jawabin a kan Aure, ta fara da bayanin menene Aure? Ta ce, Aure wata hanya ce da Shari’a ta zaba domin gudanar da rayuwar yau da gobe tsakanin namiji da mace. Hikimar Aure shi ne samun nutsuwa da ’ya’ya na gari. Malama Maimuna Abdullahi a nata jawabin ga ’yan uwa masu farin ciki da farin cikin Manzon Allah, masu bakin ciki da bakin cikin Manzon Allah, ta yi bayanin Muhimmancin Salatin Manzo (S) da falalarsa da Matsayin Sayyida Zahra (SA) a wajen Allah da Manzo (S). Sun kai ziyara wajen Mata masu yoyon fitsari, da Mata a Kurkukun cikin Birni. Sun fitar da wasu Mata albarkacin Sayyida Zahra. Sun ba da kyautar shinkafa da katan din Taliya ga wasu mutane biyu, da niyyar Allah ya kai ladan ga Shaheed Muhammad Aliy. A karshe sun gayyaci Malama Maimuna da Malaman Wahda su je Fada su gai da Sayyida Zahra (SA). Sun ba wa Mata 11 masu sunayen Matan Manzo kyauta da mai suna Amina, Babar Manzo (S) da mai suna Halimatus Sa’adiyyah wadda ta shayar da Manzo. Ranar Asabar 10/6/1434 (20/4/2013) an yi a Halkar Kurna. Sun yi a Rijiyar Lemo bayan Gidan Nasiru Ahali. Sun yi Fadak, sun zuba kayan marmari da rumfar Sayyida. Sun tanadi kayan abinci, Semovita, Shinkafa, Manja da Mankuli, Dubulan, Cincin, Albasa, Tattasai, Kubewa busasshiya, Onga, Ajino-moto, Taliya katan 9, Semovita buhu 9, Fura da Nono, Agogon bango 5, set din kofuna, Yadin Hijab, da Littatafai. Malaman Wahda, Malama Karima Abubakar, Malama Bahijjah M. Kabara, Malama Zaliha Ibrahim Musa. Malaman Wahda Maza Yarbawa Mal. Abdulganiyyu da Mal. Muhyuddeen sun yi jawabai daban-daban. Malama Maimuna Abdullahi ta yi jawabi a kan Sayyida Zahrah (SA), inda ta kwadaitar da ’yan uwa kan Mujahada da Muhimmancin yin Nafilfilin wuni da dare. Ta ce, lallai Addini yana bukatar salihan mutane ne, don haka mutum ya guji bin son ransa da karya da gulma. A kyautata aiki, a kula da ibada, karatun Alkur’ani, zikirori, dss. Ranar Litinin 12/6/1434 (22/4/2013) an yi a Halkar Tudun wada. Sun yi a tsohuwar Dakata. Sun yi Fadak da Rumfar Sayyida. Sun zuba kayan marmari, har da kunun Aya. Malaman Wahada, kamar Malama Umma Usman, Malama Binta Adam sun yi jawabai daban-daban. Wani abin sha’awa shi ne sun gayyato matasa masu shaye-shaye, don su nuna musu cewa Sayyida Gatan kowa da kowa ce, suka ba su kyaututtuka. Malama Maimuna Abdullahi ta yi jawabi a kan Sayyida kamar yadda ta saba. Sun kai ziyara Asibiti, sun kai safar hannu (Hand Gloves), Sabulu katan 1 da rigunan jarirai guda 20. Ranar Laraba 14/6/1234 (24/4/2013) an yi a Halkar Kofar Waika. Sun yi a Kofar Dawanau layin Transfomer. Sun yi Fadak da Rumfar Sayyida a hade (2 in 1). Sun yi Tamsiliyya guda biyu a kan Muhimmancin neman Ilimi da Hannunka mai sanda kan gyara Tarbiyyar Matasa. Sun ba wa yara kanana kyauta a madadin Muhsin, wanda barinsa ya zamo sanadin shahadar Sayyida. Sun bai wa wata baiwar Allah kyautar injin Taliya da Fulawa don ta yi jari. Sun ba Makarantar Allo kyautar Klin katan 2 don su raba wa Almajirai su yi wanki. Sun ba wa Gidajen Marayu Makwabta kyautar Taliya katan uku. Malaman Wahda, Malama Baraka Adam daga Darikar Tijjaniyya da Malama Zainab ta yi wa Sayyida Kirari. Malama Baraka ta yi jawabi kan Muhimmancin Hadin kan Musulmi. Malama Maimuna Abdullahi ta yi jawabi kan Sayyida. A karshe sun gayyaci Malama Maimuna da Malaman Wahda su shiga Fadak din da suka tanada. Ranar Asabar 17/6/1434 (27/4/2013) an yi a Halkar Fagge. Sun yi a Koki bayan Gidan Haj. Mariya Sunusi Dantata. Sun yi Fadak da Rumfar Sayyida. Malaman Wahada, Malama Sa’adatu da Malama Zainab Siraj sun yi jawabai daban-daban. Malama Maimuna Abdullahi ta yi jawabi a kan Sayyida. Ta fara da yi wa al’ummah sallama, masu farin ciki da farin cikin Manzon Allah, masu bakin ciki da bakin cikin Manzon Allah. Ta ce, Allah yana nuna isharori daban-daban a kan matsayin Ahlulbaiti. Duk wanda ka ga yana kin Ahlulbaiti, to ka bincika Mahaifiyarsa ta ci amanar Babansa, wato dan halas ba zai ki Ahlulbaiti ba. Sun ba wa Maigadin Makabarta Shadda. Sun tanadi Tukwane domin gyara Makabartu saboda damina. Sayyida Zahra ke nan gatan Rayayyu da Matattu. Sun je Asibitin Dawanau sun kai kayan sawa kala 25 da katan din Klin da sabulu. Wannan Maulidi shi ne Maulidin karshe a Halkokin Kano a wannan shekara. Kuma Allah ya saukar da ni’imar ruwan sama kafin a tashi daga Maulidin, wanda suka kira da Ruwan wanke Maulidai. Ranar Asabar 1/7/1434 (11/5/2013) ita ce ta zamo ranar Khatamar Maulidan, wanda muka sami halartar babbar bakuwa, Malama Zeenat Ibrahim. An yi taron a Filin Masallacin Gidan Sarkin Kano. Dimbin al’umma ne suka sami halarta. Malama Zeenat ta tunatar da al’ummah dalilin halittar dan Adam, cewa Allah ya halicce shi ne domin ya bauta masa. Daga nan ta yi bayanin cewa babban darasin da za mu koya daga rayuwar Sayyida shi ne gwagwarmayar da ta yi. Ta yaki azzaluman lokacinta. Ba ta yi shiru ba, ta dinga tunatar da al’umma. Da ba ta fito fili ta fadi gaskiya ba, ta yi shiru, to da an girmama ta girmamawar munafunci. Malama Zeenat ta kawo hadisin Manzo (S), wanda Imam Ali ya ruwaito cewa, duk wanda ya ga Azzalumi yana zaluntar mutane, ya yi shiru, Allah zai kai shi mazaunin Azzalumin. Ta ce, “amsa kiran Malam (Zakzaky) da muka yi, uzurinmu ke nan a wajen Allah. Kar mu ji cewa muna yin gwagwarmaya ne don Addini ya tabbata; nasararmu ita ce mu sami karbuwa a wajen Allah.” A karshe Malama Zeenat ta mika kyaututtuka ga Halkoki da Yankunan da suka ci gasa. (1) Fagge da yankin Durbunde. (2) Kawo da yankin Gumel. (3) Kurna da Yankin Tudunwada. A karshe ina godiya ga Allah (T), kuma ina mika godiya ga babbar Alkaliya Binta Adam (MRS BASHIR) da Amma Zulai da Amma Siyanatu, wadanda suka taimaka min da wasu bayanai. Allah ya saka da alkhairinsa. Kuma ina tawassuli da Sayyida Zahra na sadaukar da ladan wannan rubutu (TYPING) ga Mahaifina ALH. YUSUF GARBA MAITAYA. Allah ya kai ladan ga ruhinsa, ya ji kansa, ya gafarta masa, ya sa shi a ceton Sayyida Zahra da Babanta da Mijinta da ’Ya’yanta, amin.
Posted on: Tue, 25 Jun 2013 23:07:14 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015