YABON GWANI: Fasahar Marigayi Salihu Jankidi Wakar Bubakar Dan - TopicsExpress



          

YABON GWANI: Fasahar Marigayi Salihu Jankidi Wakar Bubakar Dan Shehu Bakadire Daga Ibrahim Sheme Jigon wannan waka shi ne fito da martaba da darajar Sarkin Musulmi Abubakar Na Uku (Allah ya jikan sa). Jankidi ya nuna cewa a matsayin Sultan din na shugaban al’ummar Musulmin kasar nan, to tilas ne kowane Musulmi ya bi shi ko kuma ya yi asara gobe kiyama. Ya kuma nuna cewa duk cikin sarakunan Nijeriya babu kamar sa, hatta Turawan mulkin mallaka, kai har ma da wasu kabilun da mabiyan wasu addinan, su na martaba shi. Wannan waka ta na burgewa matuka musamman yadda aka shirya baitocin ta tare da yawan maimaitawar wasu kalamai, sannan ga muryoyi da kida masu taushi. Allah ya jikan Jankidi, amin. AMSHI: “Bubakar dan Shehu, Bakadire, Na Bello sai Mahdi ko ba a so; Bubakar dan Shehu, Bakadire, Na Bello sai Mahdi ko ba a so” WAKA: Muzakkarin Sarki na Sakkwato, Halin mazajen farko yay yi, Ya hada ribar Shehu Mujaddadi, Abin da yas so yi duk yi ya kai. “Bubakar dan Shehu, Bakadire, Na Bello sai Mahdi ko ba a so; “Bubakar dan Shehu, Bakadire, Na Bello sai Mahdi ko ba a so” Gabas da yamma, kudu da arewa, Yau darajjar kowa: Sakkwato! Gabas da yamma, kudu da arewa, Yau darajjar kowa: Sakkwato! Koway yi gigi yas saki hanya, Babu girma nai nan duniya, Lahira kuma ta kucce masa. Danganen addini dan Hassan, Mai bid’ar shi ga Manzon Allah, Bai sakin hanyag ga, ta bi ya kai, Mu na nan biye! Danganen addini dan Hassan, Mai bid’ar shi ga Manzon Allah, Bai sakin hanyag ga, ta bi ya kai, Mu na nan biye! “Bubakar dan Shehu, Bakadire, Na Bello sai Mahdi ko ba a so; Bubakar dan Shehu, Bakadire, Na Bello sai Mahdi ko ba a so” Tun ran da Allah yat tchira duniya, Ba a yi taro irin Kaduna ba. Tun ran da Allah yat tchira duniya, Ba a yi taro irin Kaduna ba. Zamani nai sai shi yai kira, Kowa da kowa duk an hallara, Soja, ‘yan doka, Inyamiri, Jan Bature ya fi dari bakwai, Har da Yanyam na ta rawa ciki, Sahu biyar na masu dawaki, Sarkin Musulmi ya dardazo, Ba batun kowa sai girgiza, Wadansu na tafi, wasu girgiza, Magaji mai farai ka hwada masu: Uban sarakin duk Nanjeriya! Magaji mai farai ka fada masu: Uban sarakin duk Nanjeriya! “Bubakar dan Shehu, Bakadire, Na Bello sai Mahdi ko ba a so; Bubakar dan Shehu, Bakadire, Na Bello sai Mahdi ko ba a so” Zuwan Kaduna da an ka yi taro, Sarauniya ta gode ma kwarai. Zuwan Kaduna da an ka yi taro, Sarauniya ta gode ma kwarai. Ta yi murna, ta sara maka. Mutan Kaduna su na labari: Kwag ga Sakkwato ya gama kallo, Kayan Masar na Birnin Hausa, Wannan irin haske sai alfijir. Wannan irin haske sai alfijir. “Bubakar dan Shehu, Bakadire, Na Bello sai Mahdi ko ba a so; Bubakar dan Shehu, Bakadire, Na Bello sai Mahdi ko ba a so”
Posted on: Sat, 21 Sep 2013 21:39:38 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015