YAR-SOJA. A duk duniya ban ta6a, ganin kyakkyawa ba, kamar jamila - TopicsExpress



          

YAR-SOJA. A duk duniya ban ta6a, ganin kyakkyawa ba, kamar jamila yar-soja, kuma yarinyar ta mutu murus a kaina, nima bana yaudarar kaina ina kaunarta. Babanta komandan sojoji ne. Amma duk da haka sai ga jamila yar soja, kala min sheri, ta sanar da mahaifinta, babanta yana matukar kaunarta fiye da yanda ake zato. Sabida tsabar tsoron komanda a.s chinoz, yasa nabar dangina, mahaifana, abokaina, na gudu birnin ikko, domin tsira daga sharrin a.s chinoz. Abin ya samo asali ne lokacin dana dawo daga bautawa-kasa. Ina zaune a kofar shago na, ina kallo da karanta wata mujalla ta yan wasan kwaikwayo. Ban ankara ba, sai naga camry ta faka kadan dani, ina daga kai sai arba da yar soja, dubunnan murmushi a fuskarta, bata 6ata lokaci ba, ta 6alle murfin motar ta fito. Tayi sallama hade da murmushi. Na amsa cikin farin ciki, sannu da zuwa. Ta zauna kusa dani, turarenta ya buge ni, ta sanya farar riga matsattsiya, bakin siket, hijabi iya kafadu. Na rufe mujallal, na ajjiye a gefe. Ahmad ya kake? Kalau nake jamila na amsa. Ya sabis? Ya hanya? Na amsa mata da masha allah. Ahmad dad dina yana son ganink... Me? Me yasa? Na tambya cikin rudu. Ta murmusa, na bashi labarinka ne, kaine wanda nake son aura. Haba jamila ya zaki haka, kinsan sarai mahaifinki, bazai amince ba dani a matsayin mijin yarsa wadda yafi kauna. Jamila na dade ina son na fada miki mahaifina malamin addinine, limami, da wane ido kike zaton zai kalle ki, a matsayin wadda zan aura? Ba tun yanzu ba sha nuna miki a matsayinki na musulma bai dace ba kina irin wannan shigar... yar soja ta katse ni, yanzu de baka sona ahmad? Daman an fada mini kaifa baka sona nice kawai.... Tayi shuru, sannan ta mike ta kalle ni da fushi, ba damuwa ahmad, tana fadar haka cikin sauri ta shige motarta, ina kiranta ta shere ni. A washe gari ne na fara jin sherin data kakaba mini, a bakin kawarta, dan haka na hada komatse na, na nufi bauchi, wahalhalun dana fuskanta a can ne yasa nayi hijira, na nufi birnin gwabna, a can ne na kuma haduwa da kyakkyawa fatima, ta taimaka min ta kaini gidansu, a matsayin direba, bayan yan kwanaki sai ga yan sanda suna tuhumata da laifin kisan-kai. Fatima tana gabana hawaye yana diga daga idanuwanta, haba ahmad ya zakayi haka... Adaidai lokacin ne kiran yar soja ya shigo salula ta, duk da ina cikin sarka a garkame, kurtayen yan sanda kusa dani suna muzurai, hakan bai hanani murmusawa ba. By ahmad a baba 07055663578
Posted on: Mon, 21 Oct 2013 10:44:44 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015