Ɗazu nayi post amma har a Ahlus Sunnah se da aka samu wasu - TopicsExpress



          

Ɗazu nayi post amma har a Ahlus Sunnah se da aka samu wasu waɗanda suka ruɗe har wasu sun kafirta ni wasu sun jingina min shia, wasu kuma sun fahimta amma hassadar su ta motsa. Ga maanar abinda na rubuta ɗazu da safe: . Wata rana wani dattijo ya shigo fadar Amirul Muuminina Umar r.a, bayan Umar r.a ya tambaye shi ko ya ya wayi gari? Sai dattijo yace ya wayi gari yana mai son fitina, yana mai ƙin gaskiya, yana sallah babu alwala, kuma yanada abinda Allah baida shi! Dajin haka sai Amirul Muminina ya riƙi kolarsa, yana tuhumar mai zaisa ya faɗi waɗannan maganganu? Domin shi Umar r.a bai fahimci abinda mutumin ke nufiba. Amma sai Sayyidina Aliyu r.a yace ai wannan mutumin gaskiya ya faɗa, domin ya wayi gari yana mai son dukiyarsa da ƴaƴansa, Allah kuma Yace waɗannan fitina ne, ashe yana son fitina, sannan bayason mutuwa, Allah kuma yace magagin mutuwa gaskiya ne, ashe bayason gaskiya, sannan sallah da yace yanayi babu alwala yana nufin salati wa Annabi s.a.w, kuma yanada ƴaƴa da mata, Allah kuma bashida waɗannan. Daga nan saiyadi Umar r.a ya saki wannan dattijo yace yayi gaskiya. . Amma saboda jahilcin wasu wai wannan an zagi sahabbai aciki! Kuma wadda tayi post ɗin ƴar shia ce me cin mutuncin sahabbai! Wani harda tsinuwa! Se de ka mutu amma bazaka bakanta ni ba Inshaallahu, da har kake cewa da saurana naje nayi karatu, kuma kana ƙaryar sunnah. Mtsw
Posted on: Tue, 19 Nov 2013 21:06:24 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015