ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihin Sayyadi - TopicsExpress



          

ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihin Sayyadi Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam 2 Matsayin Wannan Tarihi Allah Tabaraka Wa Taala ya fifita tarihin maaikinsa a kan na sauran yan adam da duniya take ji da su. 1. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam shi kadai ne wanda aka haifa a cikin hasken rana, kamar yadda wani bature yake cewa. Abin nufi, babu wani abin da zaka so ka sani game da rayuwarsa wanda maabotansa ba su sanar da mu ba. Tun daga rayuwarsa ta cikin gida har zamantakewarsa da masoyansa da magabta. Kai, har abinda mutane ke boyewa na sirrin rayuwarsu, shi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam an bayyana nasa domin shi abin koyi ne ga musulmi fai da boye. Dubi yadda aka sifaita mana jikinsa kamar kana zaune a gabansa. Hatta da farin gashin da yake a gemunsa an qirge mana yawansa. Motsinsa kowane iri an bayyana shi a cikin tarihinsa. Tun daga yadda yake zama da tafiya da cin abinci da sa sutura da kawaici da magana da komai da komai. Dubi As-Shamail Al-Muhammadiyya h na Imam Abu Isa At- Tirmidhi ko kuma Zad Al-Maad na Ibnul Qayyim misali ba abin da ba zaka gani ba wanda ya danganci nasa salo na rayuwa wanda shi ne samfurin rayuwar da Allah yake so bani Adama su koya. Tambayi mabiyan annabi Isah (AS) me suka sani game da rayuwarsa? Ballantana duk sauran addinai irin na gargajiya da makamantansu! 2. Sai kuma ingancin da kaffatanin wannan tarihi yake da shi. Saboda babu na-ji-na-ji a cikinsa. Kome aka fada an san wanda ya cirato shi kuma ta ina ya cirato shi. Don haka in ka ga ana rigima kan wata magana da ta danganci rayuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam to, maabota sani ne ba su zo ba. Yanzu suna fayyace maka kowace ruwaya da matsayinta. 3. Ga shi kuma wannan tarihi ya cika ya batse ta kowace fuska. Rayuwar kowa akwai a cikinsa. Karamin yaro, maraya, matashi, dattijo, maigida, talaka, malami, mai sarauta, dan kasuwa, jagora, soja, farar hula, liman.. Kai har da dan gudun hijira bai rasa abin koyi a cikin wannan tsarkakakken tarihi. 4. Tsaftataccen tarihi ne da ba abin yasuwa a cikin sa. Ko sau daya ba zaka ji wani sharri ko zalunci ko duk wani abinda lafiyayyen hankali yake kyama ba a cikin sa. Rayuwa ce ta wanda Allah ya aiko shi don ya zama rahama ga talikai. Dubi duk kaifin adawar mutanen Makka, kai har da algungumai Yahudawan da suka yi makwautaka da shi a Madina. Ka taba jin wanda ya tuhumce shi da wata magana ko aiki mai zubar da mutunci? 5. Tare da haka kuma wannan rayuwa ce mai saukin koyi. Ba ta wuce iya ikon dan adam da aka halicce shi a kai ba. In ban da muujizoji - kamar Israi da Miiraji - mene ne dan adam ba zai iya kwaikwayon Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ba a cikin sa?
Posted on: Sun, 10 Nov 2013 23:17:53 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015