Assalamu alaikum wrahmatullah, Yan uwa, a darasinmu na - TopicsExpress



          

Assalamu alaikum wrahmatullah, Yan uwa, a darasinmu na baya, mun tsayane a hadisi na 8, cikin wannan littafi #UMDATUL_AHKAAM, a babin farko wato BABIN TSARKI, cikin yardan Allah zamu tashi kan hadisi na 9, Allah nake roqo ya sa mu fadi dai dai, yakuma kareni daga kuskure, idan aka samu nayi kuskure ko raunin fahimta, don Allah a gaggauta min gyara, domin ni Almajirine! (9) An karbo daga Amru bn Yahya Almaaziniy, daga Babansa, yace: Naga Amru bn Abil-hasan ya tambayi Abdallahi bn Zayd gameda Alwalar Manzon Allah s.a.w, sai ya sa aka kawo masa qwarya dauke da ruwa, sai yayi musu Alwalar Manzon Allah s.a.w: Bai tsoma hannayensa a ruwanba tukun, sai da ya wanke hannayensa sau uku, sannan ya sanya hannunsa cikin qwaryar, ya kurkure bakinsa, sannan ya shaqa ruwa a hancinsa, ya fyace shi, yayi hakane sau uku, tareda sake ruwa a kowanne shaqawa da kurkuran baki, sannan ya sake sanya hannunsa acikin qwaryar, ya wanke fuskarsa sau uku, sannan ya sake diban ruwa ya wanke hannayensa zuwa gwiwar hannunsa sau uku, sannan ya diba ruwa ya shafa kansa, ya faro daga qeyarsa zuwa masomin gashinsa sannan ya sake komawa qeya sau daya, sai ya wanke qafarsa. A wata ruwaya kuma Ya farone daga masomin gashinsa zuwa qeyarsa, sannan yatafi har qeyarsa, sai ya dawo da shafar daga qeyarsa zuwa inda ya soma. A wata ruwaya kuma: Munje wajen Manzon Allah s.a.w, sai muka kawo masa ruwa cikin qwaryar taasa. (10) An karbo daga Aisha (R.A) Tace: Manzon Allah s.a.w yakasan damaitawa tana burgeshi ya fara sanya takalmi da qafar dama, da soma tafiyarsa, da tsarkinsa da dukkan lamuransa s.a.w. (11) An karbo daga Naiymul Mujmir, daga Abu Hurairah r.a, daga Manzon Allah s.a.w cewa Yace: (Lallai Alummata zaa kirasu ranar Qiyamah, suna masu tambura na alamun alwala, duk wanda yasamu ikon tsawaita tambarinsa, to ya tsawaita. A cikin lafazin ruwayar Muslim kuma: Naga Aba Huraiarah yana Alwala, sai ya wanke fuskarsa da hannuwansa, har ya kusa kaiwa ga kafadarsa, sannan da yazo wanke qafa, sai ya wanketa har qwaurinsa, sanna yace: Naji Manzon Allah s.a.w yana cewa: Lallai Alummata zaa kirasu ranar al-qiyaamah suna masu tambari da alamu na tabon alwala, duk wanda yasamu daman tsawaita tambarinsa, to ya tsawaita. (11) A lafazin Muslim: Naji Masoyina s.a.w yana cewa: Inuwar Mumini a ranar qiyamah tsawon yanda yake isarda Alwala. **A Hadisi na 11 da 12, ana kwadaitarwa ne don cika alwala, wato yazamana ko ina ya ji ruwa kuma ya wanku, kalmar da akai amfani da ita a hadisin wacce na fassarata da Tambari itace (GURRAN MUHAJJAL,) a larabci, wannan in Akace Gurran muhajjal, ana nufin doki Baqi, wanda a gwiwarsa akwai zagaye kaman kobo, alamu kwanciya dakuma duqawa da yakeyi, a bisa haka, zakaga gashin wurin ya karkade yayi haske, hakanan akuyoyi sunadashi a qafarsu ta gaba, da dai wasu dabbobin, hakama Alummar Annabi s.a.w zasu tashi ran qiyama, sunada wannan tambari a fuska, da hannayensu, da qafafuwansu, sabida alwalar da sukeyi, wadannan gabobin zasu dinga haske suna sheqi! Allah ka haskaka fuskokin mu a wannan rana, ka tausaya mana a wannan yini mai firgici! Wassalamu alaikum warahmatullah. ViaMukoyi IBADA
Posted on: Mon, 25 Nov 2013 20:23:41 +0000

Trending Topics



br>
کیسه کِش گر آسیا رویای توست *** بازی
2008 Upper Deck Series 1 Baseball Detroit Tigers Team Set

Recently Viewed Topics




© 2015