ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta - TopicsExpress



          

ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam. Marubuci: Shaykh Dr. Mansur Sakkwato (Hafizahullah). ------ Fitowa Ta 21------ Maraya Dan Gatan Ubangiji Faruwar wannan abin alajabi ya sa Halima ta mayar da yaron zuwa gidan su saboda firgici da ya kama ta a daidai lokacin yana da shekaru hudu. Riwayoyin Ibnu Ishak - sarkin malaman tarihin maaiki - a nan sun dan yi tufka da warwara. Wai an ce ya shiga shekara ta uku kenan, kuma an ce ya kai shekara biyar. Mun rinjayar da ruwayar ta tsakiya saboda ta fi kusa da inganci. Amma cewa, ya a sannan ya fara shiga shekara ta uku.. Ya za ayi dan shekara biyu da watanni ya je kiwo?. A samu karin bayani a Ar-Raheeq Al-Makhtum, shafi na 68 da Talqih Fuhum Ahl Al-Athar na Ibn Al-Jauzee, shafi na 7. Shekara biyu bayan haka, sai Amina ta dauki yaronta domin ta sadar da zumuncin sa da danginsa na Madina; kawunnen mahaifin sa da zuriar su. Bayan da suka kammala wannan zumuncin ne a kan hanyar su ta dawowa gida sai Allah ya karbi baiwarsa a daidai kauyen da ake kira Abwau mai nisan kilomita 180 daga Madina. A can aka yi janaizar ta. Ita kuma Ummu Aimana ta dauko yaron Sallallahu Alaihi Wasallam ta dawo da shi Makka. (As-Siratun Nabawiyyah, na Ibn Hisham (1/68). Abdulmuttalib ya ji zafin mutuwar mahaifiyar manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam matuka, kuma ya fito fili ya bayyana ma sa haka. (Sahihus Siratin Nabawiyyah, na Ibrahim Al Ali, shafi na 56.) Daga nan kuma ya ci gaba da kula da jikansa har yana fifita shi a kan yayan cikin sa saboda tausayin sa. Shekaru biyu kacal bayan haka shi ma ajalinsa ya cim ma sa sai ya ce ga garinku. As-Sirah An-Nabawiyyah na Ibn Hisham (1/169). Haka dai zamu ga manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya tashi a cikin maraici saboda hikimar da ubangiji gwanin sarki ya tanada ma sa ta hanyar yin haka. Tarbiyyah da renon ubangiji sun ishi manzonsa ba sai ya bukaci wata kulawa daga mahaifa da kakanni ba. Ashe ba haka annabi Yusuf Alaihis salam ya tashi da farko a gaban mahaifinsa ba - annabin Allah Yaqub Alaihis salam - a cikin gatanci da niima da kulawa? To, amma me ya faru bayan haka? Sai madaukakin sarki ya raba shi da shi, kaddara ta gargada shi zuwa inda bai san kowa ba, kuma ba wanda ya san shi, ya je ya fuskanci kalubalen rayuwa iri-iri tun daga jefa shi rijiya, zuwa sayar da shi a kasuwar bayi, daga nan zuwa fitinar mata da aukawa gidan kaso, sai kuma babbar jarabawa ta samun mulki. Kai, a takaice dai ko da mahaifinsa ya gan shi - bayan sama da shekaru ashirin - ya ga annabin Allah. A ina ya samu wannan baiwa? Kuma wa ya yi tarbiyyar sa a kan ta? Allah ne da kansa ya jibinci wannan lamari kuma a kan haka ya kakkabe hannun kowa daga gare shi. Babu sauran wani ya yi tunanin cewa, iyayensa ne suka horar da shi a kan wannan daawa da yake yi. Babban darasin da ke cikin wannan shi ne, kada mu dauka cewa, yi ma yaro gata da sagarta shi shi ne abinda zai daukaka shi ko ya sanya shi a matsayi mai girma. Babu shakka idan iyaye suka kula da tarbiyyar dansu, suka koya ma sa ilimi da imani, sannan suka hada da rokon Allah to, ana fatar Allah ya shirya ma su shi.
Posted on: Mon, 02 Dec 2013 18:08:37 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015