DAGA MALAM YUSUF I GWANDA TARON DANGIN MAKARYATA AKAN SHAIKHUL - TopicsExpress



          

DAGA MALAM YUSUF I GWANDA TARON DANGIN MAKARYATA AKAN SHAIKHUL ISLAM IBN TAIMIYYA-2 KARYA TA 1: Karyar da tafi shahara a bakin ‘yan bid’a itace da’awar su cewa wai Ibn Taimiyyah na ba Allah sifofi irin na mutane. Wai yace Allah na da jiki irin na ababan halitta kamar kafa, hannu, fuska, ido da sauran su, abinda da Larabci ake kira Tajsim kuma ma wai yace Allah na kara girma, Yana kara hankali, da tunani da sauransu kamar yadda mutane ke yi. Magabata a wannan karyar kuwa sune as-Saqqaf da malaminsa Zaahid al-Kauthari da al-Habbashi al-Hurri,. Daga bisani sauran ma’abota bid’a musamman Rafidhawa suka cafa suke jagorantar sauran ‘yan bid’a wurin tallatawa. Kusan duk karyar da aka jinginawa Shaikhul Islam a wannan bangaren wadannan mutanen uku sune tushen ta. Misali dubi abinda as-Saqqaf ke fada bayan ya nakalto Imam an-Nawawi akan hukuncin da ya yanke na kafurtar duk wanda ya jingina wa Allah jiki, sai yace, “daga cikin wannan kason (masu jingina jiki ga Allah) sun hada da al-Harrani (Ibn Taimiyyah)…wanda ya tabbatar da jiki (tajsim) ga Allah a cikin litattafansa da yawa. Sabo da haka fadar sa a littafin sa mai suna (at-Ta’sis, 1/101) cewa, ‘kuma babu wuri ko daya a littafin Allah, ko a Sunnar Ma’aikin Sa, ko wani zance daga Magabatan wannan al’umma da Imaman ta cewa Shi (Allah) ba jiki bane kuma sifofin Sa ba na jiki bane (jasadiy) da suka kunshi gabobi…’ Nace : Ina rantsuwa da Allah Wanda Ya kagi sammai da kassai- wadannan maganganu naka sun kunshi jahilci da bata. Shin fadar Allah cewa, ‘babu wani abu da yake tamka a gare shi’ bata isa ta karyata akidar tajsim (danganta jiki ga Allah ba), yaa al-Harrani? Kuma shin maganganun Imaman wannan al’umma da Magabata dake musunta tashbihi basu isa ba, yaa al-Harrani?” (Daf Shubah at-Tashbih, 245-246). Ka ga fa yanda ma’abota bid’a suke yaudarar ilimi suna karkatar da maganganun bayin Allah. Alhamdu lillahi, malamai masu yawa masu kishin gaskiya da Sunnah sun gabace mu wurin bashi amsa. Misali, Shaikh Mash’hur Salman ya fada game da wannan kazafi, “Wannan magana ta fito ne daga bakin wanda bai san ma’anar adalci ba, wanda ke tambele da sha-talai-talai a cikin maganganun sa tare da danganta zargin karya akan malamai. Hakan kuwa zai bayyana ta fuskoki masu yawa: daga ciki shine cewa maganar da ya kawo ba ta Ibn Taimiyyah bace. Ibn Taimiyyah ya nakalto maganganun Ahlul Kalam ne, amma sai as-Saqqaf ya cire farkon zancen daga rubutun Ibn Taimiyyah inda yace, “Qaalu” (Suka ce)…Game da wannan mas’ala Shaikhul Islam na cewa, “Hakika kalmar jiki (al-jism), gaba (al-Arad), Mai iyaka (al-Mutahayyiz), sabbin kalmomi ne kirkirarru. Mun bayyana a wurare da dama cewa Magabata da Imamai basu ambaci kwatankwacin wannan magana ba, ko ta hanyar tabbabtarwa ko inkari ba. Alal hakika ma sun ambaci masu irin wannan ra’ayi da cewa ma’abota bid’a ne, suka kuma kyamace su”. Wannan shine matsayin Shaikhul Islam-Allah Yayi rahama gare shi- a cikin litattafan sa masu yawa., kamar misali, ‘Sharh Hadith an-Nuzul, shafi na 69-76, Majmu’ al-Fataawa, juzu’i na 3 shafi na 306-310, juzu’i na 13 shafi na 304-305, Minhajus Sunnah an-Nabawiyyah fi naqdi kalam ash-Shii’a wa al-Qadariyyah, juzu’i na 2 shafi na 134, da na 192, da na 198-200, da na 527. Hakika a Sharh Hadith nuzul Shaikhul Islam ya fada game da danganta jiki ga Allah da cewa, ‘bid’a ce a shari’ah, batanci ne ga lugga kuma sabawa ne ga hankali. Kuma lallai shari’a, lugga da hankali duk sun ci karo da wannan da’awa….yaci gaba da cewa, ‘Duk wanda ya riya cewa Ubangiji jiki ne da ma’anar abun da za’a iya rabawa, ko a shiga tsakani- to kuwa ya kai kololuwa ga kafirci da jahilci. Hakika zancen sa yafi muni akan na wanda yace Allah Ya riki da- duk da cewa makasudin maganar su na nufin cewa wani bangare na Allah Ya cire ya zama da daga gare shi” (Mujallar al-Asalah, lamba ta 4, shafuka na 54-55, da kuma littafinsa mai suna Rudud wat Ta’qubaat, shafuka na 21-23). Shima Dr. Sa’id Ramadan al- Buti a littafin sa mai suna Nadwa Ittjahat al Fiqr al-Islami, shafuka na 264-265 cewa yayi, “Mamaki kan cika mu a duk lokacin da muka ga masu tsatstsauran ra’ayin bid’a suna kafirta Shaikhul Islam. Ko su zarge shi da wai yana fadar cewa Allah jiki ne (mujassid), ni kuwa nayi naci da kwalailaita da zuzzurfan binciken littafan Shaikhul Islam ban ga wani zance ko kalma daga gare shi ba wacce ya rubuta ko ya fada wacce ke tabbatar da haka kamar yadda al-Subki da sauran su suka fada ba…abin da kawai na gani a litattafansa shine cewa, ‘Hakika Allah na da hannu kamar yadda Ya fada, Ya kuma daukaka akan Al-arshi kamar yadda Yace, kuma yana da ido kamar yadda Ya fada…”
Posted on: Fri, 11 Oct 2013 20:50:53 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015