DUK WATA WAYEWA DA BANA ADDINI BA BATA NE. Wato yanuwa mun - TopicsExpress



          

DUK WATA WAYEWA DA BANA ADDINI BA BATA NE. Wato yanuwa mun riski wata rayuwa, da tarbiyya ta lalace. Yanxu koyi da yahudu da nasara shine, wayewa, idan kay duba, zuwaga matasanmu maza da mata, zakaga gaba daya dabiunsu, da yanayin shigar su, bata addini bace ta yahudawa ce zallah, mun manta da addinin,mu, mundauko Aladun wasu munzo muna rayawa, kuma har muke ganin shine wayewa, wallahi muji tsoran Allah manzan Allah s.a.w yace mutum yana tare da wanda yakeso, kasani muddin kana koyi da wadannan mutane ranar kiyama tare zaa tasheku. Dashi, Allah yake cewa cikin suratul maidah ayata 51 yaku wadanda suka yi imani kada ku riki yahudu da nasara majibinta, sashensu majibinta sashi ne. Kuma wanda ya jibince su daga gare ku ,to lalle ne shi yana daga gare su , hakika Allah baya shryar da mutane azzalumai. Yanxu mata masu sanya hijabi da maza masu shigar sunnah sun zama abin dariya abun izgili, ana ganin kauyawa ne, Alhalin sune wayayyun, me abin wayewa a fita tsirara? Wlh tsiraici muni ne ba kyau ba Musani wadannan mutanen da muke koyi, muke irin shigarsu, muke jin wakokinsu, basu kaunar mu, burinsu Addinin Allah yayi kasa, idan kunne yaji jiki ya tsira. Allah ya shiryemu.
Posted on: Mon, 25 Nov 2013 11:20:36 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015