GORON SALLAH:SAURIN WUCEWAN LOKACI,ALAMA CE TA KAREWAN - TopicsExpress



          

GORON SALLAH:SAURIN WUCEWAN LOKACI,ALAMA CE TA KAREWAN DUNIYA(tashin kiyama):Manzon Allah S.A.W. Ya baiyana cewa:saurin wucewan lokaci,yana daga cikin kananan alamomin karewan duniya(tashin kiyama) ABIN LURA:(1)kwanan nan ake cewa:WATAN RAMADANA yayi kusan kamawa,watan yakama,ana murna yau 1 ga watan ramadana,kamar wucewar iska,wai har ramadana ya wuce,kuma yanzunnan zakaji wani ramadana ya zagayo,muna ta mamakin saurin wucewan lokaci.(2)agaskiya ba mamaki yakamata muyi tayi kawaiba,IZNA(darasi)ya kamata mu dauka,da irin wannan saurin wucewan lokacin ne,ko wannenmu zai cinye dan AJALIN DA ALLAH YA DIBA MASA,NA RAYUWA,AWANNAN DUNIYAR,sai ka wayi gari ace:YAU WANE KWANANSA YA KARE(3)ya kamata mu nitsu,mu dawo cikin hankalinmu,mu ribaci rayuwarmu,da lokacinmu,musan me muke ciki?,kuma me muke tanadawa saboda LAHIRARMU?,yanzu ne muke da dama,in muka kuskura ta kubuce mana,zamuyi nadama alokacin da nadama bata da amfani,Allah Madaukakin sarki yana cewa:ARANAN(tashin kiyama)MUTUM ZAI WA‘AZANTU,AMMA WA‘AZANTUWANSA BAZAI MASA AMFANIN KOMAI BA,ZAI CE:YA KAITONA!,INA MA,DA NA GABATAR DA AIKIN ALHERI,DON RAYUWATA TA LAHIRA?(3)Aliyyu Allah ya kara masa yarda yace:YAU(duniya)SHUKA CE KAWAI MUKEYI,GOBE(lahira)SHINE RANAN GIRBI(abinda ka shuka shi zaka girba,alheri ko sharri,babu yanda zai yiwu maka,kashuka TABA anan duniya,ranan LAHIRA kuma ka girbe GWABA,tabar da ka shuka ita zaka girba)(4)Umar Allah ya kara masa yarda yace:KUYI HISABI WA KANKU(tun anan duniya)KAFIN AYI MUKU HISABI(a lahira)(5)Allah Madaukakin Sarki ya ce:YA KU WADANDA SUKAYI IMANI,KUJI TSAORON ALLAH,KO WACE RAI TAYI NAZARI,TA DUBA,TAGA MENENE TA QADDAMAR(ta aikata)DOMIN GOBE(kiyama),KU TSARE DOKOKIN ALLAH,LALLAI ALLAH MASANI NE,DA ABINDA KUKE AIKATAWA(ZAI BAKU LABARIN AIYUKANKU,ARANAN KIYAMA,KUMA ZI SAKA MUKU DA IRIN AIKINKU).(
Posted on: Sun, 11 Aug 2013 18:36:08 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015