NAJERIYA TA KAFA TARIHI A GASAR KARATUN ALQURANI TA - TopicsExpress



          

NAJERIYA TA KAFA TARIHI A GASAR KARATUN ALQURANI TA DUNIYA! INA TAYA KANAWA MURNA, KUMA DAGA YAU NA DAINA YIWA KANAWA TSIYA DOMIN ASHE KANAWA TAGUN AL-QURNI KUNE GWANAYE. KUSAN BAKYAU YIWA MAHADDACIN AL-QURANI TSIYA. KANAWA A YAFE NI A yau ne aka rufe gasar karatun da kasashe a ko ina fadin duniya ke halarta, KABIRU ABUBAKAR daga jahar Kano ne ya zo na daya (1st position) a matakin Hizb Sittin da Tafsir, kuma na farko da ya taba samun wannan matsayin daga Najeriya tun shigarta a jerin kasashen da ke halartar gasar. Daga bisani NAZIRU ABUBAKAR SULAIMAN daga jahar Sokoto wanda ya wakilci Najeriya a matakin Hizb Sittin (tilawa) ya zo na biyar (5th position). Sannan ABUBAKAR daga jahar Jigawa wanda shima ya wakilci kasar Najeriya a matakin Hizb Arbain ya zo na uku (3rd position). Muna taya wadannan zaratan matasa da suka daga darajar kasarmu Najeriya a cikin kasashen duniya murna da farin cikin samun matsayi. Muna fatar samun nasara a wasu shekaru masu zuwa, Amin. YAN SOKOTO DA YAN JIGAWA KUMA BAA BARKU A BAYA BA, INA MUKU MURNA. Muhsin
Posted on: Mon, 02 Dec 2013 06:52:41 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015