NAZARI AKAN SAKACIN GWAMNATINMU TA NIGERIA - TopicsExpress



          

NAZARI AKAN SAKACIN GWAMNATINMU TA NIGERIA : ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Yan uwa ku dubi lamarin cutar nan ta EBOLA da yadda take yaduwa kuma take kisa cikin gaggawa, sannan ka dubi ta yadda ta shigo mana nan Qasar.. Sannan idan ka dubi irin yadda Gwamnatinmu ta Nigeria take da sakaci akan manyan alamura, to dole abin ya Qara baka tsoro. Domin kuwa alamomi sun nuna cewa tun yanzu Gwamnatinmu ta Nigeria ta fara nuna alamar cewa ba zata iya killace Mutanen da suka harbu da cutar EBOLA ba.. Mai yasa suka kyale wannan Nurse din ta tsallake wajen da aka killaceta, har ta tafi Enugu taje ta harbi Mutane 21?? Abisa dukkan alamu da kyar ne in Gwamnatin zata iya killacesu a tsaftataccen waje, ta samar musu da Ishashen abinci da kulawa ta musamman ga iyalansu da sauran wadanda suke Qarkashinsu. Duk mutumin da aka killaceshi akwai bukatar akula masa da iyalansa wadanda nauyinsu yake wuyansa. Sannan akula da abincinsa, suturarsa, Makwancinsa, da sauran abubuwan rayuwa. WANI ABUN FARGABAN MA SHINE: Wasu daga cikin Jamian Gwamnati zasu iya amfani da wannan damar domin AZURTA KANSU ta hanyar karkatar da kudaden da Gwamnati zata ware don wannan shaanin izuwa Aljihunsu ko asusun ajiyar bankinsu. (Kamar yadda ake zargin suna aikatawa akan shaanin tsaro a arewacin Nigeria). Mu dai Musulmai mun yarda da Qarfin addua.. Kuma bamu da wani matakin da zamu iya dauka sai ita. Don haka shawarar ZAUREN FIQHU ita ce mu yawaita maimaita HASBUNALLAHU WA NIIMAL WAKEEL aduk lokacin da muka tuno da zancen cutar nan ta Ebola, da kuma guraben Sallolinmu da lokutan Zikirin Allah na safiya da maraice. Alqurani ya nuna mana cewar duk wanda ya fadi HASBUNALLAHU WA NIIMAL WAKEEL babu wani abinda zai cutar dashi.
Posted on: Thu, 14 Aug 2014 15:00:37 +0000

Trending Topics



="min-height:30px;">
IF YOUR NAME IS IN THE LIST SEND A MASSAGE TO THIS NUMBER
Familia Araneta check this out! PALM BEACH VILLAS Pasay
Spent the evening and late evening driving the back country roads
Panasonic Power Board Part # Vep71197A CHECK PRICES NOW! >>
The very best in Cubic Zirconia Rings, pendants, earrings and
Depo 334-1109R-AS1 Dodge Neon/SX 2.0 Passenger Side Replacement

Recently Viewed Topics




© 2015