Ranar laraba da karfe daya da mintuna talatin da uku 1:33 munyi - TopicsExpress



          

Ranar laraba da karfe daya da mintuna talatin da uku 1:33 munyi posting na tambaya cewa "MENENE ABU MAFI FARINCIKI DA ALLAH YAIWA DAN ADAN MUSULMAI KA KAFURAI? Aganina abu mafi farin ciki da ubangiji yaiwa dukkan bil adama shine "BOYE MUSU RANAR MUTUWARSU" domin da ace mutum yasan ranar da zaya mutu to kullum kwanan duniya sabon lissafi zayayi yau fa saura kwana kasa na mutu, wani ma kila saura kwana 10 ko 20 ne ya mutu. To daganan kuma fa ba sauran kwanciyar hankali da farin ciki. Babu abun da dan adam yafi tsana arayuwarsa irin mutuwa, domin yau da wani zayazo yace wane yaufa saura kwana kasa ka mutu to fa baka da abokin jin haushi irin wannan wanda yazo maka da albishir na mutuwarka. Wannan yasa nace ba wani abu mafi farin ciki gurin dan adam kamar "BOYE MASA RANAR MUTUWARSA DA ALLAH UBANGIJI YAYI" #Azeezah
Posted on: Fri, 04 Oct 2013 23:19:31 +0000

Recently Viewed Topics




© 2015