TARIHIN SHEHU IBRAHIM INYASS Tarinhin shehul-islam - TopicsExpress



          

TARIHIN SHEHU IBRAHIM INYASS Tarinhin shehul-islam sheikh ibrahim inyass Shine sheikh ibrahim dan shehu Adullahi Inyass. An Haifeshi Agarin (daiban yasin) gari ne da mahaifinsa yakafa a kaulakh dake kasar senegal. Ranar alhamis Bayan la`asar 15 rajab ,1900. Hijra 1320. Yatashi akan kularwar mahaifinsa, ya Haddace Al- Qurani a Hannun mahaifinsa Acikin kananan shekaru Ya wallafa littafi A rana daya yana da shekaru 21 aduniya. Ya turo ilimi Zahiri dana Badini Har Yazama baida Tamka a Fagen ilimi a duk duniya. Yazama Gagara Misali acikin son Manzo Allah (SAN) da yabonsa. Faiyar da Shehu Ahmadu Tijjani mai Darika yai Bushara da Zuwanta ta Bayyana a Hannunsa a HiJra 1348. Yayi HIJra daga garinsu Kaulaka Ranar Safiyar Sallah 1939. Yatafi HaJJin Farko 1937 kuma a wannan shekara ce ya hadin da sarkin kano shehu Abdullahi Bayaro (sarkin AlhaJi) wanda yai Asalin shigowar shehu Nigeria Shehu yai wallafa littafai Ba’ adadi daga cikin akwai, shahararren Duwaninsa da Kashiful ILbas da Ruhul –Adat . Yaba″YAya 75 MAZA da MATA ya rayu shekaru 75 yarasu A Asibitin London Rana 15 ga Rajab.An rufeshi A Madinarsa a Gaban Masallacinsa Raularsa ta Zama Abin Ziyara a Kowa ne Lokaci A na Masa Lakabi da Shehul Islam Abu Ishaq Sahibul Faidha Inyass. Allah yakaramashi Karama Amin
Posted on: Wed, 24 Sep 2014 10:51:27 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015