INGANTACCIYAR HANYAR SAMUN TSARO KAI TSAYE DAGA ALLAH - TopicsExpress



          

INGANTACCIYAR HANYAR SAMUN TSARO KAI TSAYE DAGA ALLAH (SWT) QUL-HUWA DA FALAQI DA NASI yaushe ake son musulmi yake karanta su? AMSA Lokuta ne guda 3-4 wanda ake son mutum musulmi akullum karya kuskura ya wuce ba tare daya karanta wadannan surori ba. 1-SAFIYA DA YAMMACI Annabi (saw) yace من قالها ثلاث مرات حين يصبح وحين يمسي كفته من كل شيء Ma‘ana Annabi yace duk wanda ya karanta QUL-HUWA,FALAQIDA NASI sau 3 da safe, sau 3 da yamma, zasu zame masa kariya/garkuwa daga dukkan komai Abu-dawood (3/322) Sahih s/Tirmixi (3/182) 2-BAYAN KO WANI SALLAN FARILLA. Hadisin Abu-dawood da nisa‘i sun tabbatar da cewa annabi yana karanta wadannan surori 3 abayan ko wani sallah (ta farillah) Abu-dawood (2/86) Sunan Nisa‘i (3/68) Amma a sallolin magrib da asuba sau 3-3 annabi yake karantawa. Fathul-bary (9/62) 3-LOKACIN KWANCIYA BARCI Nana Aisha (r.a) tace annabi ya kasan akullum yazo kwanciya barci yakan hada hannayenshi biyu sannan ya karanta wadannan surorinnan 3 sai ya shafe jikinshi dasu. Bukhari (9/62) MUslim (3/1723) YAN-UWA MUYI RUKO DA KARANTA WADANNAN SURORI, DOMIN SHAKKA BABU ZAMU SAMU TSARON ALLAH MADAUKAKI Allah yasa mu kiyaye
Posted on: Mon, 21 Oct 2013 11:27:27 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015