A WATA JAMIA CE AKA DAURA AURE CIKIN WASA KUMA YA TABBATA DA - TopicsExpress



          

A WATA JAMIA CE AKA DAURA AURE CIKIN WASA KUMA YA TABBATA DA GASKE Wata budurwa ce mai suna ZAINAB da wani saurayi mai suna AHMAD.. Ba saurayi da budurwa bane amma suna mutunci a tsakaninsu har Ahmada yana baiwa zainab ajiya kudi,sai rannan an zauna group discusion suna final exam,akwai mutane dayawa a wurin,sai Ahmad ke tambayar zainab amma zainab da mungama school aure zakiyi ko,sai tacemasa. Eh,sai yace inama nizaki aura sai tace,cab aini kayimin yaro da aure,sai yace inafa nayi yaro kice nakawo sadaki kigani,duk mutanen wajen na saurarensu har ana dariya,sai tace to kawo sadakin duk acikin wasa fa,sai yace nawa ne sadakin tace dubu goma,yace dauka cikin kudina dake hannunki saura dubu biyu kenan Sai kuwa zainab tace to dahaka ma a daura aure yanzu akace eh a daura,wani abokin Ahmad ace bari yaje a sawo alawa matsayin goron daurin aure,nan da nan sai gashi yadawo da jakar alawa,aka rabawa mutanen dake wurin anata dai raha da dariya,sai kuwa akace toke zainab ina waliyyinki sai ta nuna wani cousin brother dinta tace gashi,sai akace kai Ahmad ina waliyyinka shima ya nuna wani dan uwansa yace gashi,ai kuwa nan take aka daura aure cikin sigar daurin aure aka shafa fatiha duk wadanda ke wurin suka shaida. To ashe akwai wani Akramakallahu can gefe yana kallonsu kuma yana sauraren duk abunda sukeyi sai dai bai rabasu da uffan ba,sai da suka gama ana wasa da dariya har sun tashi zasu watse sai kuwa mutumen nan yataso yace Assalamu Alaikum,suka amsa,yace yan uwa ina daga gefe ina saurarenku kun daura auren Zainab da Ahmad cikin wasa kun tashi,to abunda baku sani ba shine Aure ya dauru ya tabbata tsakanin Zainab da Ahmad,ba shakka zainab ta tabbata matar Ahmad idan kuma baku gasgata zancena ba zaku iya zuwa wurin duk wani malami da kuka yarda dashi ku tambaya,ai baa wasa da daurin aure,aifa har sun dauki maganar malamin nan shirme,akaje wurin wani islamic lecturer aka tambayeshi shima yace ba shakka aure ya tabbata, Bayan sun gama exams duk basu yarda ba da suka koma gida dama unguwar su daya suka fadawa mahaifansu abunda yafaru,akaje wurin malami har ukku duk maganar daya ce cewa aure ya tabbata,ai kuwa zainab me zatayi sai aza hannu saman kai kuka take ba arziki gashi tanada wanda takeso har iyayensu sun shiga maganar,ai kuwa Ahmad sai murna,kuma akace Ahmad ya saketa yace shikam bai san zancen ba,aka kida aka raya yace wallahi bazai saki ba, iyayensa ma suka goya masa baya,zainab ta. Rame ta kode amma ina bakin alkalami yariga ya bushe,kawai akayi biki aka kai amarya gidan Ahmad.............. Tambayata agareku malaman wannan gida shin dagaske Aurensu ya tabbata kuwa? Wannan fatawar tayi kuwa????????
Posted on: Fri, 14 Feb 2014 16:19:49 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015