Hakika So dafine, So gubane, So Masifa ne, ga wanda Allah ya - TopicsExpress



          

Hakika So dafine, So gubane, So Masifa ne, ga wanda Allah ya jarabce shi da shi. So wata yanace da kan Makantar da idanun Masoya, ga barin ganin laifin juna. So shi ne abu mafi girma da yake iya sarrafa zuciyar kowanne irin Mutum. So wani haske ne, da yake haskaka zukatan Masoya. So na gaskiya, shi ne ginshikin dorewar Soyayya. So na gaskiya shi ne, ka so Mutum don Allah, ba don wani dake tare da shi ba, ko abin hannunsa ba. So kan iya zama linzami, ga duk wani da ya tsinci kansa a tarkon sa. So wani Marurune, mai yawan azabtar da zukatan Masoya. So wani tsirone da kan iya tsirowa a zuciyar duk wanda ya ga dama. So ba ruwansa da Kyau, Kudi, Ilmi, Mulki, Cancanta ko Nasaba. Babu shakka Soyayya ita ce jindadin rayuwa ga wanda ya dace da ita. Lafazin kauna shi ne, abu mafi girma da ya fi tausasa zukatan Masoya. Ba zaka taba sanin menene farin ciki ba, ko bakin ciki ba sai lokacin da kake Soyayya. Soyayya tafi komai dadi, amma tafi komai azabtar da zukata. Soyayya ita ce tushen kafuwar aure, da wanzar da zaman lafiya ga Masoya. Soyayyar da aka gina ta da tubalin gaskiya, ba zata taba rushewa ba. Rashin gina Soyayya a kan tafarkin gaskiya, shi ne kan haifar da yawan mutuwar Aure da rashin zaman lafiya. Soyayya ita ce ginshikin jindadi, amma wani lokacin takan zama Illa. Rashin sanin darajar So, kan haifar da yawan rugujewar Kauna prince of love
Posted on: Mon, 21 Oct 2013 06:00:25 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015