Kyaftin din kwallon kafar Nigeria Vincent #Enyeama ya ce ya yi - TopicsExpress



          

Kyaftin din kwallon kafar Nigeria Vincent #Enyeama ya ce ya yi imanin kasar za ta iya lashe gasar kofin duniya da zaa yi badi a Brazil. Super #Eagles ce kungiyar Afrika ta farko da ta samu tikitin shiga gasar bayan ta doke Ethiopia 4-1 a wasanni biyu. Sai dai wannan yakini na Enyeama ya sabawa tarihi da kuma yanayin wasan #Nigeria na baya bayan nan. Rabon Nigeria da cin wasa a gasar duniya tun nasarar da ta samu a kan #Bulgaria a 1998 kuma ita ce karo na karshe da Super Eagles ta fito daga rukuninta. A tarihin gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya, kasashen Afrika uku ne kacal suka taba kai wa matakin daf da na kusa da na karshe: #Cameroon a 1990, #Senegal a 1992 da #Ghana a 2010 yakuke ganin wanan magana ta #enyeama ?? Via #Ibrahim DTM
Posted on: Mon, 18 Nov 2013 11:48:40 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015