LABARI DA DUMIDUMINSA: RARIYA NEWSPEPAR: Cigaba Da Yajin - TopicsExpress



          

LABARI DA DUMIDUMINSA: RARIYA NEWSPEPAR: Cigaba Da Yajin Aikin ASUU: Kungiyar Dalibai Za Ta Shirya Tarzoma Kungiyar dalibai ta kasa tana shirin gudanar da babban zanga-zanga na kasa baki daya a wani mataki na tilasta Gwamnatin Tarayya da kuma Kungiyar Malaman Jami’o’i kan su kawo karshen yajin aikin da malaman ke yi a yanzu. Shugaban Kungiyar Daliban, Yinka Gbadebo ya ce, a halin yanzu kungiyar na kokarin bin duk wata hanyar sulhu na rokon bangarorin biyu inda ya ce, kada a dauka cewar kungiyar ba ta nuna damuwa kan halin da ake ciki ba a mai¬makon haka a cewarsa, suna ci gaba da tuntubar bangarorin da abin ya shafa. Ya ce, sun rubutawa kwamitin bunkasa jami’o’in na Gwamnan jihar Binuwai, Mista Gabriel Suswan kuma idan ba su samu wani gamsasshen amsa daga kwamitin ba, za su bada wa’adin mako guda daga kuma za su fara gudanar da zanga- zangar. A wani labari kuma, Shugaba Jonathan ya bukaci Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) da su kawo karshen wannan yajin aikin da suke yi a yanzu tun da Gwamnatin Tarayya ta rigaya ta saki Naira bilyan 30 don bi¬yan malaman kudaden alawus-alawus da suke ikirarin suna bin gwamnati. Shugaban ya yi wannan ki¬ran ne a lokacin kaddamar da wasu ayyuka a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke garin Owerri a jihar Imo. Shugaban, wanda Ministar Ilimi, Farfesa Rukayya Rufa’i ta wakilta ya ce, shi bai ga dalilin da malaman jami’o’in za su ci gaba da wannan yajin aikin ba. Shugaba Jonathan ya kuma nemi shugabannin jami’o’i da su mayar da hankali ga ban¬garen bincike don samun ci ga¬ban kasar inda kuma ya jaddada muhinmancin kula da wadannan ayyuka, matakin da ya ce,na daga manufar gwamnati na samar da ingantaccen ilimi a kasa. Anasa bangaren, Shugaban Jami’ar, Farfesa Chidozie Asiaba¬ka ya nuna jin dadinsa bisa kammala wadannan gine-ginen inda ya ce, sun taimaka matuka wajen farfado da darajar jami’ar. Ya ce, ta hanyar tallafin da jami’ar ke samu daga Asusun Bunkasa Man¬yan Makarantu, jami’ar na da manyan dakunan koyar da darasi guda 1,000 da makamantansu. Admin:002
Posted on: Fri, 30 Aug 2013 20:31:18 +0000

Trending Topics



30px;">
Question 2: Is Jesus really God? Well when you think about it you

Recently Viewed Topics




© 2015