Alhaji Ghali Maaji Abdulhameed (Maajin Madangala). Mahaifinsa - TopicsExpress



          

Alhaji Ghali Maaji Abdulhameed (Maajin Madangala). Mahaifinsa shine marigayi Alhaji Maaji Dahuwa Abdulkadir. An haifi Ghali a Cikin garin Azare, yayi karatun primary a Day primary school Azare, yayi secondary a FGC Azare, yayi degree na farko a BUK Kano. Ghali yayi aikin Banki na shekaru 14 har sai da ya kai matsayin manager a Kano, yayi aiki da Hon. Auwalu Abdu a matsayin PA, yanzu haka yana aiki a National Assembly Ofishin Duputy Speaker a matsayin mai bashi shawara ta fannin siyasa. Daga shekarar 2011 zuwa yau Ghali yayi aikace-aikace da dama don cigaban mutanen Katagum Constituency. Daga cikin irin ayyukan da Ghali yayi sun hada da: 1. Tonon Rijiyoyi sama da 20 a kauyuka daban-daban kamar su Buskuri, Chinade, Madaci, Gangai, Madara, bulkachuwa, Ragwam d.s. 2. Gyaran famfunan Burtsatse sama da 15 a wurare daban-daban cikin kasar Katagum. 3. Rufin Masallaci da karasa aikin sa a Cikin garin Ragwam. 4. Sayen tabarmai sama da 400 a masallatai daban-daban. 5. Tallafawa kungiyar marayu. 6. Tallafawa yan makaranta. 7. Tallafawa kananan asibitoci da Magani. 8. Daukan nauyin kiwon lafiyar mata 100 na tsawon shekara guda 1 a FMC Azare. 9. Kawo Transformers guda 3, kofar fada Azare, matsango, da k/kaji Azare.
Posted on: Sun, 24 Aug 2014 13:06:33 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015